Rashin Aure: Malamin Addini Zai Gudanar da Addu'o'in Musamman ga Mata da Maza

Rashin Aure: Malamin Addini Zai Gudanar da Addu'o'in Musamman ga Mata da Maza

  • Rashin aure ya yi yawa a tsakanin matasan Najeriya yayin da malami ya shirya gudanar da addu'a ta musamman
  • Fasto Enoch Adeboye zai jagoranci addu’o'i na musamman ga matasa marasa iyalai da masu neman haihuwa a watan Nuwamba
  • An ce addu’ar ta samo asali daga yawaitar bukatun aure domin taimaka wa ‘yan mata da maza marasa aure, da mata masu neman karuwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Babban Limamin Cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye, ya yi magana kan matasa marasa aure.

Faston ya bayyana cewa zai gudanar da addu’o'i na musamman ga matasa marasa aure da iyalai masu neman haihuwa.

Fasto zai yi addu'o'i ga gwauraye maza da mata
Malamin addinin Kirista, Fasto Enoch Adeboye yayin wa'azi a coci. Hoto: Pastor EA Adeboye.
Source: Facebook

Dalilin yin addu'o'i ga marasa aure a Najeriya

Enoch Adeboye ya sanar da haka cikin wata sanarwa da Mataimakinsa na musamman kan harkokin gudanarwa, Fasto Oladele Balogun, ya fitar a Lagos, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani bayan Tinubu ya sassauta hukuncin Maryam Sanda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce addu’ar ta samo asali ne daga shawarwari, kuma za ta mayar da hankali kan matasa da manya da ba su da aure, da mata masu neman haihuwa da iyalansu.

Adeboye ya nuna cewa bayanan gwamnati sun tabbatar da cewa sama da kashi 40 cikin 100 na manya a Najeriya ba su da aure a halin yanzu.

Za a yi addu'o'i ga masu son aure a Najeriya
Fasto Enoch Adeboye yana huduba a coci. Hoto: @PastorEAAdeboye.
Source: Twitter

Yawan mabukatan aure na karuwa a Najeriya

Faston ya ce wannan rukuni yana kara yawa, kuma suna neman samun aure, yayin da mata masu neman haihuwa a duniya ke fuskantar kalubale tare da addu’a da fatan samun nasara.

Ya ce:

“Wannan ya nuna yadda ake samun karuwar masu bukatar aure, masu neman haihuwa da waɗanda ke sa ran haihuwa, waɗanda adadinsu ya kai miliyoyi a duniya, sun haɗa da iyalai masu addu’a don samun ‘ya’ya.
“A fadin duniya, inda RCCG ke da rassa sama da kasashe 190, waɗannan rukuni suna cikin manyan sassan al’ummar coci, an haɗa su da bangaskiya, fata da addu’a.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya fadi matsalar sulhu da 'yan bindiga, ya yi gargadi

"Ya ƙara da cewa ana gayyatar mahalarta daga ko’ina cikin duniya domin shiga wannan taro na musamman da zai sauya rayuwa tare da taimakon Ubangiji.”

A ina za a yi addu'a ga marasa aure?

Za a gudanar da addu’o’in ne yayin bikin godiya a ranar 2 ga watan Nuwambar 2025 a Babban Hedikwatar RCCG, Ebute-Metta da ke Lagos, da karfe 8:00 na safe a cewar Peoples Gazette.

Limamin Kiristan ya jaddada cewa dukkan mabiya na duniya za su iya shiga ta yanar gizo, yayin da wadanda ke kusa da Lagos ake karfafa musu guiwa su halarta a zahiri domin samun albarka.

Fasto Adeboye ya fadi ranar mutuwarsa

Mun ba ku labarin cewa Fasto Enoch Adeboye ya bayyana cewa ya hango cewa zai mutu a wata ranar Lahadi bayan ya gama ibada, kuma ya ci sakwara.

Shugaban cocin na RCCG ya ce zai mutu ba tare da wata rashin lafiya ba, don a cewarsa, ciwo ba shi ne alamar mutuwa ba.

Ya shawarci Kiristoci su dage wajen neman bukatunsu a wajen Almasihu, ya kuma yi magana kan yin rayuwa a cikin talauci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.