Gwamna Bala Ya Tura Sunayen Sababbin Kananan Hukumomi 29 da Ya Kirkiro ga Majalisa
- Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya kirkiro sababbin kananan hukumomi 29 a jihar Bauchi domin inganta harkokin mulki
- Hakan ya biyo bayan amincewar Majalisar Dokokin jihar Bauchi da kuma rattana hannun da Gwamna Bala Mohammed ya yi kan dokar
- Majalisar Bauchi ta aika wasika ga Majalisar Tarayya domin neman amincewa da kafa wadannan sababbin kananan hukumomi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi, Nigeria - Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya rattaba hannu kan dokar kafa ƙarin kananan hukumomi 29 a jihar.
Wannan mataki na zuwa ne bayan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta amince da bukatar gwamnan na kirkiro wadannan kananan hukumomi guda 29.

Source: Twitter
Bauchi ta aika sako ga Majalisar Tarayya
Sai dai a wata takarda da Daily Trust ta samu, mukaddashin mataimakin magatakardan Majalisar Dokokin Bauchi, Musa Yerima, ya aika da wannan kuduri ga Majalisar Tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Musa Yerima ya tura kudirin ta hannun Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki domin neman amincewar majalisar kasa wajen kirkiro sababbin kananan hukumomi 29 a Bauchi.
A halin yanzu, Jihar Bauchi ta na da kananan hukumomi 20 da kundin tsarin mulkin 1999 ya amince da su, kamar yadda Guardian ta rahoto.
Idan aka ƙara sababbi 29, hakan zai sai adadin kananan hukumomin Bauchi ya kai 49, tare da kimanin mutane miliyan 10 da ake hasashen suna zaune a jihar.
Abin da Bauchi ta bukata daga Majalisa
A cikin wasikar da ya rubuta wa Sanata Barau Jibrin, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Gyaran Tsarin Mulki, Musa Yerima ya ce:
“Ina farin cikin sanar da ku cewa Majalisar Dokokin Bauchi ta amince da dokar kafa ƙarin kananan hukumomi 29 a Jihar a shekarar 2025.”
Ya bayyana cewa sababbin kananan hukumomin za su kasance na wucin gadi har sai Majalisar Tarayya ta amince da su kamar yadda Sashe na 8(5) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ya tanada.
Musa Yerima ya ƙara da cewa:
“An aiwatar da wannan doka bisa ga tanadin Sashe na 100, sakin layi na 3 na Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Najeriya (na 1999, da aka yi wa gyara).”
Sunayen sababbin kananan hukumomin Bauchi
Da wannan doka, Bauchi ta zama ɗaya daga cikin jihohi a Arewa maso Gabas da suka ɗauki matakin faɗaɗa tsarin mulki a kananan hukumomi domin ƙara inganta shugabanci da samar da ci gaba a mataki ma fi kusa da jama'a.
Sunayen sababbin kananan hukumomin su ne:
1. Balma
2. Bauchi ta Gabas
3. Bauchi ta Yamma
4. Beshongo
5. Bula
6. Burra
7. Chinade
8. Dagauda/Jalam
9. Disina
10. Dogon Jeji/Jurara
11. Dass ta Yamma
12. Gadau
13. Galambi
14. Ganjuwa ta Gabas
15. Girawa
17. Gwana
18. Isawa
19. Jama'a
20. Karkara
21. Lame
22. Lere
23. Madara
24. Sade
25. Sakuwa
26. Saye
27. Udubo
28. Yankari
29. Zungur.

Source: Twitter
Gwamnan Bauchi ya nada Sarkin Zaar
A wani rahoton, kun ji labarin cewa gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar da nadin Birgediya Janar Marcus Kokko Yake (mai ritaya) a matsayin Sarkin Zaar na farko a tarihi.
Wannan nadi na zuwa ne bayan Gwamna Bala Mohammed ya kirkiro sababbin masarautu 13 a jihar Bauchi domin inganta ayyukan sarakuna.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa hakan ya haifar da zanga-zanga a Karamar Hukumar Tafawa Balewa, inda wasu mutanen Sayawa suka nuna ba su yarda da nadin ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


