Juyin Mulki: Yadda Sojojin da aka Tsare Suka 'Tona Asirin' Tsohon Minista, Timipre Sylva
- Sababbin bayanai sun kara bulla a kan yadda aka alakanta tsohon Ministan man fetur, Timipre Sylva da kokarin juyin mulki
- Rahotanni sun ce hukumomin tsaro a kasar nan da suka hada da DIA, tare da EFCC da NFIU ne suka gano kudin da aka so amfani da su
- Kuma bayanai daga sojojin da ke hannun hukumomi sun alakanta tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Sylva da yunkurin kifar da gwamnati
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Sababbin bayanai sun bayyana a kan yadda jami’an DIA tare da hadin gwiwar hukumar kula mu'amalar kudi NFIU da EFCC suka yi aiki don gano kudin da aka so amfani da su wajen juyin mulki.
Rahotanni sun nuna cewa binciken ya kai ga asusun tsohon gwamnan Jihar Bayelsa kuma tsohon karamin Ministan man fetur, Cif Timipre Sylva.

Source: Facebook
Jaridar The Sun ta wallafa cewa bayanai sun ce Timipre Sylva da daga cikin wadanda ake zargi a gaba-gaba wajen daukar nauyin shirin kifar da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Yadda sojoji suka tona asirin Timipre Sylva
Rahoton ya ce wasu majiyoyi sun bayyana cewa wasu jami’an soja da aka kama da hannu a shirin juyin mulkin ne suka tona asirin Timpre Sylva, wanda ya ki dawowa Najeriya daga kasar waje.
DIA ta nemi taimakon EFCC da NFIU domin bibiyar asusun bankuna da mu’amalar kudi da ake zargin ana amfani da su a shirin juyin mulkin da ake kullawa.

Source: Facebook
A cewar rahoton, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ki gaskata lamarin da fari, sai da aka kawo masa hujjoji daga hukumomin uku sannan ya yarda cewa an yi ƙoƙarin kifar da gwamnati.
Wani babban jami’in tsaro ya tabbatar cewa an gano wasu makudan kudi da aka ware domin sayen jiragen leken asiri domin samun bayanai.
Sannan an kara ware wasu kudin domin sayo makamai na zamani don aiwatar da juyin mulkin ba tare da amfani da sojoji da yawa ba.
Sharri aka mani, cewar Timipre Sylva
Tsohon gwamnan, wanda yanzu yake wajen ƙasar, ya bayyana sharri kawai ake masa, amma ba shi da hannu a wani yunkuri na juyin mulki.
A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman, CIf Julius Bokoru ya fitar, ya ce labarin juyin mulkin duk ƙarya ce da wasu masu makirce suka ƙirƙiro domin lalata masa suna kafin zaɓen 2027.
A kalamansa:
“Wasu ‘yan siyasa 'yan son kai ne suka kulla wannan sharri saboda suna ganin Sylva babban cikas ne ga burinsu."
Ya tabbatar cewa jami’an tsaro sun ziyarci gidan Sylva da ke Abuja, inda suka lalata kadarorinsa, amma ba su bayyana dalilin wannan farmaki ba.
Ya kara da cewa:
“Sylva ɗan dimokuraɗiyya ne na gaskiya, wanda ya gina rayuwarsa a kan imani da tsarin dimokuraɗiyya tun daga shekarun 1990.”
Sojoji sun bibiyi kudin shirya juyin mulki
A baya, kun ji cewa wasu rahotanni sun bayyana cewa, rundunar soji ta fara bibiyar yadda wasu asusun banki suka karɓi kuɗi Naira biliyan 45 da ake shirin juyin mulki da su.

Kara karanta wannan
Minista a zamanin Buhari, Sylva ya musanta hannu a shirin yi wa Tinubu juyin mulki
An ce an bi diddigin hanyoyin kuɗin zuwa hukumar raya yankin Neja Delta, inda ake ci gaba da binciken kwakwaf domin samun karin bayanai a kan dalilin fitar da kudin.
Hukumomin tsaro suna ci gaba da aiki, kuma ana sa ran za su bankado karin bayanai a kan batun yunkurin juyin mulkin da hukumomin tsari suka ce babu shi da farko.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

