Ajali Ya Gitta: Saurayi Ya Mutu daga Zuwa Zance Wurin Budurwa a Jihar Yobe

Ajali Ya Gitta: Saurayi Ya Mutu daga Zuwa Zance Wurin Budurwa a Jihar Yobe

  • Wani matashi dan shekara, 20, Jibrin Sa'idu Lamido ya rasa rayuwarsa da ya je fira wurin budurwarsa a kauyen Gurdadi, jihar Yobe
  • Rahotanni sun nuna cewa ana zargin wani mutumi da har yanzu ba a gano bayanansa ba shi ne ya kashe saurayin a daren Talata
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Yobe, DSP Dungus Abdulkarim ya ce jami'ai sun fara bincike don gano abin da ya faru

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe - Mazauna ƙauyen Gurdadi da ke cikin Ƙaramar Hukumar Yusufari Jihar Yobe sun shiga yanayin tashin hankali bayan wani rikicin soyayya da ya faru ranar Talata.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe wani saurayi dan shekara 20, Jibrin Sa’idu Lamido, a kauyen lokacin sa'ilin da ya je zance wurin budurwarsa da daddare.

Kara karanta wannan

Shirin juyin mulki: Sojoji sun bi diddigin N45bn zuwa hukumar raya Neja Delta

Jihar Yobe.
Hoton taswirar jihar Yobe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Aminiya ta ruwaito cewa bayanan farko sun nuna cewa abin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na tsakar daren Talata, lokacin da Jibrin ya ziyarci, Saratu Gata, mai shekaru 22, a ƙauyen Kalameri domin zance.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kashe saurayi kan soyayya

Wata majiya daga kauyen Gurdadi ta bayyana cewa Jibrin na cikin hira da sahibarsa Saratu, kwatsam wani mutumi da ba a san ko waye ba ya dura gabansu a daren.

A cewar majiyar, mutumin ya dauki budurwar daga wurin kuma ta bi shi babu gardama, sannan ya kalubalanci saurayin da ya biyo su idan ya cika namiji.

Lamarin ya rikide zuwa tashin hankali mai muni bayan Jibrin ya bi su, inda ake zargin mutumin ya ciro adda ya sari saurayin a wuya.

Wata majiya daga jami'an yan sanda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce:

“An yi hanzarin daukar Jibrin zuwa Asibitin Kumaganam domin ceton ransa, amma likita ya tabbatar da cewa rai ya yi halinsa tun kafin a isa."

Kara karanta wannan

2027: Gwamnonin Arewa 3 na tsaka mai wuya game da barin PDP zuwa APC

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ya wallafa rahoton wannan lamarin a shafinsa na yanar gizo

'Yan sandan Yobe sun fara binciken lamarin

Rundunar yan sanda reshen jihar Yobe ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta na mai cewa tuni aka mika gawar saurayin ga iyayensa domin yi masa jana'iza da birne shi.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da cewa jami'ansu sun fara bincike kan lamarin.

Jami'an yan sanda.
Hoton wasu jami'an rundunar yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Ya ce jami'an 'yan sanda sun fara kokarin cafke mutumin da ake zargi da aikata wannan danyen aiki domin ya girbi abin da ya shuka bayan kammala bincike.

Wannan al'amari ya tada hankulan mazauna kauyen Gurdadi, wadanda suka nuna damuwa da alhinin mutuwar saurayin daga zuwa wurin zance.

Masoya sun daura wa kansu aure a Kano

A wani labarin, kun ji cewa wasu masoya, Aliyu Abdullahi, mai shekaru 22, da Khadija, mai shekaru 16, sun daura wa kansu aure a jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa saurayi da budurwar sun yi haka ne bayan iyayensu sun ki yarda da batun aurensu.

Kara karanta wannan

Sabanin yadda ake zato, Sanusi II ya fadi dalilin Jonathan na fasa cire tallafi

Hukumar ta jihar Kano bayyana cewa auren da yaran suka daura bai cika ka’idojin shari’ar Musulunci ba, don haka aka yanke shawarar soke shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262