Atiku Ya Yi Martani bayan Tinubu Ya Sassauta Hukuncin Maryam Sanda
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya soki gwamnatin Tinubu bayan ta sake duba afuwar da ta yiwa wasu 'yan Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta sanar da yafewa wasu 'yan kasar nan kusan 200, daga ciki har da wadanda suka aikata laifuffukan kisa da safarar kwaya
- Amma bayan jama'a sun yi ca a kan batun, Shugaba Tinubu ya sake waiwayar wadanda aka yi wa afuwa, tare da yin gyare-gyare
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, bayan ta sake nazari a kan yiwa Maryam Sanda afuwa.
Kotunan kasar nan sun yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa bayan an kama ta da laifin kashe mijinta a gidansu da ke babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan
Lauya ya fadi lokacin da ya ragewa Maryam Sanda a kurkuku sakamakon afuwar Tinubu

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Atiku Abubakar ya yi tir da yadda ya ce gwamnati tana aiki kafin ta yi tunani a kansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya sake dura a kan Tinubu
Daily post ta wallafa cewa Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu bayan ya janye afuwar da aka bai wa Maryam Sanda da wasu masu laifuffukan miyagun kwayoyi da satar mutane.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce gwamnatin Tinubu wannan na nufin cewa gwamnatin bata nazari kafin yanke hukunci.

Source: Facebook
Ya ce:
“Tinubu ya soke afuwar da ya bai wa masu safarar kwaya da masu garkuwa da mutane ne kawai bayan ‘yan Najeriya sun yi ihu da ƙorafi. Wannan ba hikima ba ce, abin kunya ne.”
Atiku ya tambayi gwamnati me yasa ta amince da afuwar waɗanda aka yanke musu hukunci kan manyan laifuffuka.
Jerin sunayen, wanda ya jawo cecekuce sosai a Najeriya ya kunshi mutanen da suka yi kisan kai yayin aikata mugayen ayyukansu.

Kara karanta wannan
Abin boye ya fito fili: Gwamnatin Tinubu ta faɗi dalilin sassauci ga Maryam Sanda
Atiku: Gwamnati ba ta tausayin jama'a
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya kara da cewa wannan lamari ya nuna rashin hangen nesa da rashin tausayawa al'ummar da aka zulunta.
Ya ƙara da cewa:
“Idan mutane ba su yi magana ba, da yau ‘yan ta’adda da masu safarar kwaya sun samu ‘yanci bisa sa hannun shugaban ƙasa. Me ya sa aka rubuta sunayensu a cikin waɗanda za a yi wa afuwa? Kuma ina Ministan Shari’a lokacin da wannan abin ya faru?”
Gwamnatin Tinubu ta sassautawa Maryam Sanda
A wani labarin, kun ji cewa Ministan Shari’a kuma Lauyan Babban Ƙasa, Lateef Fagbemi, SAN, ya bayyana cewa gwamnati ta sake duba afuwan da aka yiwa Maryam Sanda.
Ya bayyana cewa an dauki matakin domin domin tabbatar da cewa waɗanda suka amfana da tsarin afuwan Shugaban kasa sun cika ka’idojin doka da matakan da shari’a ta tanada.
Fagbemi ya bayyana cewa daga cikin jerin fursunoni 86 da aka rage hukuncinsu akwai Maryam Sanda, wacce aka yanke mata hukuncin kisa a 2020 saboda kashe mijinta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng