Za a Zamantar da Ilmi a Najeriya, Malamai za Su Daina Taba Alli daga 2027

Za a Zamantar da Ilmi a Najeriya, Malamai za Su Daina Taba Alli daga 2027

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daga shekarar 2027 za a daina amfani da allo mai aiki alli a makarantu
  • Ministan ilimi, Dr Olatunji Alausa, ya ce gwamnati za ta samar da allon na musamman a dukkan makarantu
  • Ya kuma bayyana cewa binciken shekara-shekara na makarantu zai koma tsarin fasahar zamani daga 2026

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa daga shekarar 2027 ba za a sake amfani da allo mai aiki da alli ba wajen koyarwa a makarantu.

Za a daina amfani da allo mai aiki da alli ne domin za a maye gurbinsa da sababbin allunan zamani a duk faɗin ƙasar.

Allo a makaranta
Allo mai aiki da alli da na zamani a aji. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tribune ta rahoto cewa ministan ilimi, Dr Olatunji Alausa ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa a Abuja.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta kare sanya harajin 15% da zai jawo tashin farashin fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya jaddada kudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na rage gibin fasaha a sashen ilimi.

Ya ce gwamnati na da cikakken shiri na tabbatar da cewa dukkan makarantu za su samu kayan koyarwa na zamani domin tabbatar da ingantaccen ilimi da ya dace da tsarin duniya.

Shirin raba wayoyi da allon zamani

Ministan ya bayyana cewa tuni gwamnati ta fara rarraba manyan wayoyin hannu (tablet) fiye da 60,000 ga ɗalibai a jihohin Adamawa, Oyo da Katsina karkashin shirye-shiryen Airtech da BESDA.

A cewarsa, ana sa ran ƙarin na’urori 30,000 za su iso nan ba da jimawa ba:

“Mun ƙaddamar da sabon allon zamani mako biyu da suka gabata,”

Ya kara da cewa:

“Burinmu shi ne daga shekarar 2027, kowace makaranta a Najeriya za ta mallaki wannan allon.”

Ya ce wannan mataki ne da zai tabbatar da cewa duk yaro zai samu ingantaccen ilimi, ko a gari yake ko a karkara, ba tare da la’akari da matsayin iyayensa ba.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito fili: Gwamnatin Tinubu ta faɗi dalilin sassauci ga Maryam Sanda

Fa'idar aiki da allon zamani a makarantu

Alausa ya bayyana cewa allon zamani zai maye gurbin allon da ya ke aiki da alli a makarantu, wanda zai bai wa malamai damar amfani da bidiyo da sauransu.

Ya ce tsarin zai taimaka wajen sa ɗalibai su rika fahimtar darasi ta hanyar kallon hotuna, sauraron bayani da yin hulɗa kai tsaye da malamai.

Ministan ilimin Najeriya
Ministan ilimi wajen kaddamar da allon zamani a Legas. Hoto: @DrTunjiAlausa
Source: Twitter

Ya ce wannan tsarin fasaha zai ba da dama ga malamai su koyar ta hanyar kirkire-kirkire, kuma ɗalibai su fi fahimta cikin sauki.

A ranar 10 ga Oktoban 2025 ministan ya raba allunan zamani 1,000 kyauta a jihar Legas, kamar yadda ya wallafa a X.

Wasu matsalolin ilimi a Najeriya

Ministan ya ce gwamnati ta fara amfani da bayanan gaskiya wajen tsara manufofin ilimi, musamman domin shawo kan matsalar yaran da ba su zuwa makaranta.

Ya bayyana cewa sama da yara miliyan 24 da suka gama firamare ba su kai gaba zuwa matakin sakandare ba, bisa bayanan da aka samo daga NEMIS.

Kara karanta wannan

Mutanen birnin tarayya za su zauna a duhu, TCN ya fadi dalilin dauke wuta a Abuja

A cewarsa, daga cikin yara miliyan 30 da aka musu rijista daga jihohi 21, yara miliyan 6 kacal ne suka kai matakin sakandare.

Legit ta tattauna da malamar makaranta

Wata malamar makaranta mai koyar da Physics a jihar Gombe, Nusaiba Bala Adamu ta ce samar da allunan zamani zai inganta ilimi.

Malamar ta ce:

"Zai taimaka wa malamai da dalibai saboda dama duniya ta rungumi irin tsarin, sai dai idan za a kawo shi dole sai an horar da malamai kan yadda za su yi aiki da shi.
"Yanayin kasar kuma kowa ya san babu wuta sosai, wani wurin ana shafe wata shida babu wuta.
"Ga kamar allon zai yi aiki da intanet, akwai bukatar data. da dai sauran matsaloli. Bana tunanin hakan mai yiwuwa ne, amma da za a yi, zai taimaka."

An kawo sababbin darusa a makarantu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta fitar da jerin darusan da za cigaba da koyarwa a makarantun sakandare.

Ma'aikatar ilimi ta tarayya ce ta fitar sabon tsarin ta kuma bayyana cewa zai fara aiki a zangon karatun 2025/2026.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya gargadi Tinubu kan cin bashi, ya tuna abin da ya fadawa Buhari

Daga cikin darusan da aka kawo akwai yaren kasashen waje kamar China da kuma yaren komfuta irinsu Python, JavaScript, AI, da dai sauransu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng