Hukumar KSPHCMB Ta Gano Sababbin Nau'ukan Cutar 'Polio' 4 a Jihar Kano
- Hukumar KSPHCMB ta gano sababbin nau'ukan cutar shan inna, wacce aka fi sani da Polio guda hudu a jihar Kano
- Shugaban hukumar, Farfesa Salisu Ahmad ya ce idan ba a dauki mataki ba, cutar na iya yaduwa a Kano duk da an taba kawar da ita a baya
- Jami’ar Rigakafi ta Jihar Kano, Hajiya Sa’adatu Ibrahim ta roki iyaye su ci gaba da kai 'ya'yansu wurin rigakafi a lokutan da suka dace
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnatin Kano ta tabbatar da bullar nau'ikan cutar shan inna watau Polio har guda hudu a fadin jihar.
Hukumar Kula da Lafiyar Jama'a a Matakin farko ta Jihar Kano (KSPHCMB) ce ta tabbatar da gano wadannan sababbin nau’ikan cutar shan inna guda huɗu.

Source: Facebook
Hukumar ta yi gargadin cewa idan ba a ci gaba da yin rigakafi a kai a kai ba, cutar na iya sake yaduwa duk da an taba kawar da ita a Kano, in ji rahoton Daily Trust.
Kano ta gano nau'ukan cutar Polio 4
Shugaban KSPHCMB, Farfesa Salisu Ahmad, wanda Daraktan Kula da Cututtuka na Hukumar, ya wakilta, ya bayyana haka ne a taron da aka shirya a ranar Laraba domin bikin Ranar Polio ta Duniya a Kano.
Ya ce tsakanin 2013 zuwa 2015, Kano ce cibiyar yaduwar cutar a Najeriya, amma ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da abokan hulɗa, an sami nasarar kawar da ita.
Sai dai ya bayyana cewa “aikin bai ƙare ba,” domin an sake gano sababbin nau’ukan cutar guda huɗu, inda ɗaya daga cikinsu ke kan bincike a dakin gwaje-gwaje.
Da take bayani kan halin da ake ciki game da Polio, Jami’ar Rigakafi ta Jihar Kano, Hajiya Sa’adatu Ibrahim, ta ce an gano sababbin nau’ikan cutar biyu a cikin kananan yara a ƙauyuka.
A cewarta, sauran nau'ika biyu aka gano su a cikin ruwan datti a wasu yankuna na birnin Kano, in ji rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan
EFCC ta bayyana wasu 'yan kasuwa da ake zargi da daukar nauyin ta'addanci a Najeriya
Yadda za a kawar da cutar a Kano
Hajiya Sa’adatu ta ce:
“Tsaftar muhalli kaɗai ba ta wadatar wajen kawar da cututtukan da rigakafi ke iya magance su ba. Dole ne mu ci gaba da tabbatar da cewa ana yi wa ’ya’yanmu rigakafi.”
“A 1988, an sami mutane 350,000 da suka kamu da cutar Polio a duniya. Amma ta hanyar rigakafin yara akai-akai, an kawar da cutar a Indiya da Afghanistan, kafin daga baya a kawar da ita a Najeriya.
"Dole mu ci gaba da sa ido da yin rigakafi domin tabbatar da cewa an kawar da cutar gaba ɗaya.”

Source: Getty Images
Kano ta gargadi jama'a kan bullar zazzabi
A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Kula da Cututtuta ta Kano (KNCDC) ta gargadi mutane da su dauki matakan gujewa kamuwa da zazzabi mai sa zubar da jini.
Hakan na zuwa ne bayan rahoton da Hukumar Kula da Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) ta fitar cewa akwai wasu mutane biyu da ake zargin sun kamu da zazzabin mai tsanani a Abuja.
KNCDC ta bukaci mazauna Kano su yi taka tsan-tsan tare da bin matakan tsafta domin kaucewa kamuwa da wannan zazzabi a Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

