Annabi SAW: An Zargi Shehin Darika da Batanci a Kaduna, an Mika Korafi ga Uba Sani
- Wata kungiya ta kai ƙarar wasu malamai biyu bisa zargin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W) a jihar Kaduna
- Malamai 16 ne suka sanya hannu kan ƙorafin tare da roƙon gwamnatin Uba Sani ta ɗauki mataki cikin gaggawa
- Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da karɓar ƙorafin tare da alƙawarin bincikar lamarin domin kauce wa tashin hankali
Jihar Kaduna – Gamayyar malamai ƙarƙashin inuwar Concerned Ulama of Sunnah ta kai ƙarar wasu malamai biyu bisa zargin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W) a Kaduna.
Ƙungiyar ta bayyana cewa irin wadannan maganganu na iya haifar da tashin hankali idan ba a ɗauki mataki a kan lokaci ba.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka gabatar da korafin ne a wani bidiyo da Ibrahim Shehu Giwa ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan
Tinubu ya cire Maryam Sanda da wasu 'yan safarar kwaya cikin wadanda ya yiwa afuwa
Batanci: An zargi malamai 2 a Kaduna
A cikin ƙorafin, malaman sun bayyana cewa ayyukan waɗannan malamai biyu suna ƙeta alfarmar Annabi (S.A.W) kuma suna iya haifar da rikici a cikin al’umma.
Sun roƙi gwamnatin Jihar Kaduna da ta gayyace su domin tattaunawa idan ya zama dole, ko kuma ta dakatar da su daga irin wadannan wa’azozin.
Masu ƙorafin sun gargaɗi cewa idan aka yi sakaci wajen ɗaukar mataki, hakan na iya jawo tashin hankali wanda gwamnati ba za ta iya shawo kansa cikin sauƙi ba.

Source: Facebook
Malaman da aka shigar da korafi a kansu su ne Shehu Mansur Kaduna da aka zarga da batanci da kuma Usman Dangungun mai da'awar Kur'ani zalla.
Kiran malaman ga hukuma a Kaduna
Ƙungiyar Concerned Ulama of Sunnah ta ce akwai buƙatar hukumomi su ɗauki wannan batu da muhimmanci saboda yana da alaka kai tsaye da ka’idojin Musulunci.
Sun kuma ambaci shari’o’in addinin Musulunci da kalaman manyan malamai da ke nuna cewa ɓatanci ga Annabi babban laifi ne.
A cikin ƙorafin, malaman sun jaddada cewa Kaduna ta yi fama da rikicin addini a baya amma an shawo kansu da kyar.
Don haka, sun bukaci gwamnati ta yi aiki cikin gaggawa domin hana rikici da rarrabuwar kai a tsakanin al’umma.
Martanin gwamnatin Kaduna kan korafin
A martanin da ya yi, jami'in hukumar addini a jihar Kaduna, Tahir Umar Tahir, ya tabbatar da karɓar ƙorafin daga hannun malaman.
Rahoton Aminiya ya nuna cewa ya ce an karɓi korafin a madadin gwamnan Jihar, Sanata Uba Sani, kuma za a gudanar da cikakken bincike a kan batun.
Tahir U. Tahir ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin mabiya addinai daban-daban.
Izala ta yi ta'aziyyar rasuwar Sarkin Hausawa
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban malaman kungiyar Izala na kasa, Dr Ibrahim Jalo Jalingo ya yi ta'aziyyar rasuwar Sarkin Hausawan Makurdi.
Sarkin Hausawa, Alhaji Rayyanu Sangami ya rasu ne bayan rashin lafiya kasa da kwana 40 da samun mulki.
Shugaban malaman ya bayyana cewa marigayin ya bayar da gudumawa a ayyukan kungiyar tare da rokon Allah ya jikansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

