Shirin Juyin Mulki: Sojoji Sun Bi Diddigin N45bn zuwa Hukumar Raya Neja Delta
- Sojojin Najeriya sun gano wasu biliyoyin Naira da aka fitar daga asusun raya Neja Delta a cigaba da bincike kan batun juyin mulki
- Ana zargin wasu manyan jami’an gwamnati da sojojin da ke tsare da hannu wajen raba kudin domin su cimma manufarsu
- Sai dai hukumar tsaro ta ƙaryata cewa akwai shirin juyin mulki, tana mai cewa ana yin binciken ne saboda dalili na daban
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Rahotanni sun bayyana cewa binciken da rundunar sojojin Najeriya ke gudanarwa kan zargin yunkurin juyin mulki ya kai ga hukumar raya Neja Delta.
Binciken sojojin ya gano cewa an fitar da kuɗi da ya zarce Naira biliyan 45 daga asusun hukumar NDDC domin cimma wannan manufa.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa an aika kudin ga wasu manyan 'yan siyasa da kuma wasu sojoji da aka tsare da subisa zargin hannu a yunkurin kifar da gwamnati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka fara gano batun juyin mulki
A farkon watan Oktoba, jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa an tsare jami’an soji 16 bisa zargin shirya juyin mulki domin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Sai dai rundunar soji ta ƙaryata wannan zargi, inda kakakinta, Birgediya Janar Tukur Gusau ya bayyana cewa ana binciken jami’an da ake tsare ne kan wasu laifuffuka da suka shafi aiki ba juyin mulki ba.
Rahotanni da dama sun kuma nuna cewa an yi samame a gidan tsohon gwamnan Bayelsa kuma tsohon ministan man fetur, Timipre Sylva a Abuja, bisa zargin alaƙa da batun juyin mulki da aka ce babu shi.
Batun juyin mulki ya jawo fargaba a NDDC
Bayan gano wannan kuɗi, jami’an DIA sun fara bincikar manyan jami’an NDDC kan asalin kuɗin, waɗanda suka ci gajiyarsa da kuma yadda aka yi amfani da su.
Wannan lamari ya tayar da hankula a shelkwatar NDDC, inda wasu ke tsoron binciken na iya haifar da zuzzurfan bincike kan mu’amalolin kuɗi na hukumar gaba ɗaya.
Wasu majiyoyi daga cikin NDDC sun shaidawa jaridar cewa yawancin manyan jami’an hukumar sun shiga fargaba tun bayan da aka fara gayyatar wasu daga cikinsu don amsa tambayoyi.

Source: Twitter
Wani ma’aikaci ya ce:
“Tun bayan da aka ji labarin gayyatar manyan jami’an, ofishin ya zama cike da tsoro. Mutane suna takatsantsan da motsinsu da kalamansu.”
An bayyana cewa akwai wani babban aikin gina gabar ruwa da aka bai wa tsohon gwamna a yankin Kudu maso Kudu, wanda kudinsa ya kai N45bn, kuma wani ɓangare daga cikinsa ana zargin ya shiga asusun wasu daga cikin sojojin da ake tsare.
Kakakin hukumar NDDC, Seledi Thompson-Wakama, ya ƙi yin bayani kan batun lokacin da aka tambaye shi halin da ake ciki kan gano yadda aka kasafta kudin.

Kara karanta wannan
Mintuna 30 a tsakani, jirage sama 2 na rundunar sojoji sun yi hatsari, sun fada teku
Sojoji sun yi kame kan shirin juyin mulki
A baya, mun wallafa cewa jami’an leƙen asirin soja sun kama wani Darakta-Janar na wata hukuma ta gwamnatin tarayya daga yankin Kudu maso Kudu a kan batun juyin mulki.
Rahotanni sun nuna cewa ana tuhumar wannan jami’in da aika kuɗi masu yawa zuwa ga tsohon Ministan man fetur, Timipre Sylva wanda ake ganin yana da hannu a shirin.
An kuma ji cewa an kai samame a gidan Timipre Sylva da ke Abuja, inda jami’an tsaro suka kama ƙaninsa da direbansa, yayin da tsohon ministan ke ƙasar waje.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

