Abin Boye Ya Fito Fili: Gwamnatin Tinubu Ta Faɗi dalilin Sassauci ga Maryam Sanda
- Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi SAN, ya bayyana dalilin sassauci ga Maryam Sanda da sauran wadanda aka daure
- Fagbemi ya ce gwamnatin Tinubu ta yi rangwame a hukuncin wasu fursunoni 86 ciki har da Maryam Sanda
- Kotu ta yankewa Maryam hukuncin kisa a 2020 bayan ta kashe mijinta, amma yanzu an mayar da hukuncin zuwa shekara 12
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - A kwanakin baya, gwamnatin Bola Tinubu ta yi afuwa ga mutane 175 ciki har da Maryam Sanda wanda ya jawo magana.
A yau Laraba 29 ga watan Oktobar 2025, gwamnatin ta sake fitar da sanarwa kan sabon sunayen da aka fitar da yan sauye-sauye.

Source: Twitter
Dalilin sake nazarin sunayen su Maryam Sanda
Ministan Shari’a kuma Lauyan Babban Ƙasa, Lateef Fagbemi, ya bayyana dalilin da yasa Shugaba Bola Tinubu ya sake nazarin sunayen, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an sake duba jerin domin tabbatar da cewa waɗanda za su amfana sun cika ka’idojin doka da matakan shari’a da suka dace.
Fagbemi ya tabbatar da cewa aikin ya kammala, kuma shugaban ƙasa ya amince da jerin sunayen na karshe na waɗanda za su amfana da sassaucin.
A cewarsa, wasu daga cikin waɗanda aka fara ba da shawarar sun kasa cika sharudda, an cire su, wasu kuma an rage musu hukunci bisa adalci da tausayi.
Cikin jerin fursunoni 86 da aka rage musu hukunci akwai Maryam Sanda, matar ɗan tsohon shugaban PDP, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a 2020.
Tun bayan haka ta kwashe shekara shida da watanni takwas a gidan yari na Suleja kafin afuwar shugaban ƙasa ta rage mata hukunci zuwa shekaru 12.

Source: Facebook
Dalilin duba yanayin Maryam Sanda
Gwamnati ta bayyana cewa an yi hakan ne bisa tausayi da jin kai ga ‘ya’yanta, kyakkyawar ɗabi’arta, da yadda ta zama abin koyi ga sauran fursunoni.

Kara karanta wannan
Tinubu ya cire Maryam Sanda da wasu 'yan safarar kwaya cikin wadanda ya yiwa afuwa
Haka kuma, wasu fursunoni da ke da hukuncin rai da rai saboda laifukan miyagun kwayoyi da kisan kai an rage musu hukunci zuwa shekaru 15 zuwa 20.
Fagbemi ya ce Tinubu ya yi hakan don daidaita adalci da jin kai, tare da tabbatar da cewa tsarin shari’a na Najeriya ya dace da ƙa’idar duniya, cewar Channels TV.
Ya ƙara da cewa an umarci a mayar da ofishin kwamitin afuwar shugaban ƙasa daga Ma’aikatar Harkokin Musamman zuwa Ma’aikatar Shari’a.
Har ila yau, shugaban ƙasa ya umurci Ministan Shari’a da ya samar da sababbin ƙa’idoji domin tabbatar da cewa wadanda suka cancanta kawai ke amfana.
Fagbemi ya gode wa ‘yan Najeriya saboda haƙuri da fahimta, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da kare mutuncin ɗan adam da tsaron ƙasa.
Mahaifin Bilyaminu ya magantu kan afuwar Tinubu
Kun ji cewa mahaifin marigayi Bilyaminu Bello, Alhaji Ahmed Bello Isa ya yi magana bayan afuwar shugaban kasa Bola Tinubu.
Dattijon ya ce ya amince da afuwar da Shugaba Tinubu ya yi ga Maryam Sanda, yana mai cewa ya dade da yafewa.
Ya ce daukar fansa ba zai dawo da ɗansa ba, amma yafiya na kawo zaman lafiya, yana mai kira da a bar komai ga Allah SWT.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

