Minista a Zamanin Buhari, Sylva Ya Musanta Hannu a Shirin Yi wa Tinubu Juyin Mulki
- Tsohon Karamin Ministan Man Fetur, Timipre Sylva ya musanta hannu a shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
- Sylva, tsohon gwamnan jihar Bayelsa na daya daga cikin wadanda ake yada jita-jitar cewa su na da hannu a shirin juyin mulki
- Mai magana da yawunsa, Julius Bokoru ya ce labarin ba gaskiya ba ne, wasu yan siyasa ne suka kirkira don bata wa Sylva suna
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bayelsa - Tsohon Karamin Ministan Man Fetur, Cif Timipre Sylva, ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa yana da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan
Abin boye ya fito fili: Gwamnatin Tinubu ta faɗi dalilin sassauci ga Maryam Sanda
Mai taimaka wa tsohon ministan kan harkokin yada labarai da hulɗa da jama’a, Cif Julius Bokoru, ya karyata jita-jitar da ke cewa Sylva na da hannu a wani yunƙurin juyin mulki.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa labarin ƙarya ce tsagwaronta da wasu ‘yan siyasa masu son zuciya suka ƙirƙira, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Sylva ya musanta hannu a shirin juyin mulki
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Bokoru ya zargi wasu ‘yan siyasa da ke kwadayin mulki a 2027 da yada jita-jitar juyin mulki saboda su na ganin Sylva a matsayin babban cikas ga burinsu.
Ya bayyana cewa waɗannan ‘yan siyasa sun fara kokarin ɓata suna da ƙage saboda girman Sylva a fagen siyasa da kwarjinin da yake da shi a idon jama’a, wanda ke tona asirin manufarsu ta son kai.
Bokoru ya ce Sylva ɗan dimokuraɗiyya ne na gaskiya, wanda ya nuna cikakken goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatinsa.
Tsohon ministan na tare da Tinubu
Ya tunatar da cewa a baya-bayan nan, Sylva ne ya jagoranci APC a Jihar Bayelsa wajen amincewa da shugabancin Tinubu a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Kara karanta wannan
Tinubu ya cire Maryam Sanda da wasu 'yan safarar kwaya cikin wadanda ya yiwa afuwa
Julius Bokoru ya ce:
“Duk da cewa Hedikwatar Tsaro ta karyata jita-jitar juyin mulki a Najeriya, yana da muhimmanci a fayyace cewa Cif Timipre Sylva, CON, ba shi da wani hannu ko masaniya game da wani yunƙurin juyin mulki.
"Sylva ɗan dimokuraɗiyya ne, wanda tafiyarsa ta siyasa tun daga majalisar dokokin tsohuwar jihar Ribas zuwa gwamnan Bayelsa, ta kasance bisa tsarin doka da yardar jama’a.”
Sojoji sun kai samame gidan Slyva?
Bugu da kari, Bokoru ya tabbatar da cewa wasu da ake zargin dakaru ne daga hedkwatar tsaron Najeriya sun kai samame gidan tsohon Ministan na Abuja, inda suka lalata kayayyaki.

Source: Twitter
Ya ce jami’an ba su bayar da wani dalili ko shaidar izini na wannan farmaki da suka kai gidan Sylva ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
"A lokacin samamen, Sylva da matarsa ba su cikin ƙasa, domin yana Birtaniya don duba lafiya, sannan zai wuce Malaysia domin halartar wani taron ƙwararru," in ji shi.
Sojoji sun kama wani Darakta-Janar
A baya, kun ji labarin cewa sojojin Najeriya sun kama Darakta Janar na wata hukuma da ake zargi da hannu a kulla shirin kifar da gwamnatin Tinubu.
Wata majiya ta shaida cewa Darakta Janar ya aika kuɗi masu yawa zuwa ga Timipre Sylva da ake zargin yana da alaka da shirin juyin mulki.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojojin sun kuma kai samame gidan tsohon ministan fetur, Timipre Sylva duk da ba su same shi ba amma sun cafke kaninsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
