Bayan Soke Afuwa, Tinubu Ya Sassauta Hukuncin Kisan da Aka Yanke Wa Maryam Sanda
- Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya canza tunani kan afuwar da ya yi wa Maryam Sanda, matar da ta kashe mijinta
- Bola Tinubu ya sassauta hukuncin da aka yanke wa Maryam daga kisa ta hanyar rataya zuwa daurin shekaru 12 a gidan yari
- An yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya ne bayan kama ta da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello a gidansu da ke Abuja
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya soke afuwar da ya yi wa Maryam Sanda, matar da aka yanke wa hukuncin kisa bayan ta kashe mijinta a shekarar 2017.

Kara karanta wannan
Abin boye ya fito fili: Gwamnatin Tinubu ta faɗi dalilin sassauci ga Maryam Sanda
Tun farko dai sunan Maryam Sanda ya bayyana a jerin waɗanda aka shirya sakin su daga gidan yari a farkon watan nan sakamakon afuwar da Shugaba Tinubu ya masu.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa bayan da jama’a suka nuna ɓacin ransu kan sakin Maryam Sanda, fadar shugaban kasa ta janye jerin sunayen gaba daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, wanda ke jagorantar kwamitin da ya bada shawarar afuwar, ya bayyana cewa za a sake duba jerin sosai kafin a amince da shi.
Tinubu ya sassauta wa Maryam Sanda
A cikin sabon jerin da aka fitar a yau Laraba, 29 ga watan Oktoba, 2025 sunan Maryam Sanda ya bayyana a rukunin wadanda aka “rage wa zaman ɗaurin rai da rai zuwa hukunci mai sauƙi.”
Bisa haka, Shugaba Tinubu ya sassauta hukuncin kisa ta hanyan rataya da aka yanke mata zuwa ɗaurin shekaru 12 a gidan yari.
Hakan dai ya nuna cewa Maryam Sanda za ta kara shekaru biyar nan gaba a gidan yari kafin a sake ta, bayan ta yi shekaru bakwai a baya.

Kara karanta wannan
Tinubu ya cire Maryam Sanda da wasu 'yan safarar kwaya cikin wadanda ya yiwa afuwa
Abin da ya faru da Maryam Sanda
Shari'ar Maryam Sanda kan laifin kashe mijinta ta hanyar caka masa wuka a lokacin husuma a gidansu da ke Abuja yana daga cikin shari’o’in kisan aure mafi shahara a tarihin Najeriya.
An gurfanar da ita a gaban Babbar Kotun Abuja, inda ta dage cewa ba ta aikata laifin da ake tuhumarta na kashe mijinta, Bilyaminu Bello ba.
Bayan doguwar shari’a da ta jawo hankalin ƙasa baki ɗaya, Mai Shari’a Yusuf Halilu, a watan Janairu 2020, ya same ta da laifi kuma ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Tun daga lokacin take tsare a gidan gyaran hali na Suleja, inda ta shafe shekaru shida da watanni takwas kafin sabon matakin rage hukuncinta da Shugaba Tinubu ya dauka.
A halin yanzu, Tinubu ya sassauta wa Maryam Sanda daga hukuncin kisa ta hanyar rataya zuwa shekaru 13 a kurkuku, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Source: Facebook
Tinubu ya soke afuwar mutane 50
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sake nazari kan mutanen da ya yi wa afuwa bisa laifukan da suka aikata.
A sabon jerin sunayen da fadar shugaban kasa ta fitar, an lura cewa Tinubu ya soke afuwar da ya yi wa mutane 50 ciki har da Maryam Sanda da wasu dillalan kwaya.
Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi SAN, ya ce babu wanda aka saki tukuna, kuma akwai karin bayanai game da jerin sunayen.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
