Lakurawa: Sabon Hafsan Sojojin Kasa Ya Sha Alwashi kan 'Yan Ta'adda
- Sabon hafsan sojojin kasa ya bayyana a gaban majalisar dattawa domin tantance shi biyo bayan nadin da shugaban kasa ya yi masa
- Manjo Janar Waidi Shaibu ya bayyana irin nasarorin da ya samu a manyan mukaman da ya rike a cikin rundunar sojojin kasan Najeriya
- Hakazalika, sabon hafsan sojojin ya sha alwashi kan 'yan ta'addan Lakurawa wadanda ke kai hare-hare a wasu jihohin Arewa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Babban hafsan sojojin kasa (COAS), Manjo Janar Waidi Shaibu, ya sha alwashin kan 'yan ta'addan kungiyar Lakurawa.
Manjo Janar Waidi Shaibu ya yi alkawarin cewa rundunar sojojin kasan Najeriya za ta yi maganin kungiyar ta’addanci ta Lakurawa da ke kai hare-hare a sassan Arewacin kasar nan.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta ce Manjo Janar Waidi Shaibu, ya bayyana hakan ne yayin zaman tantancewa da majalisar dattawa ta gudanar a ranar Laraba, 29 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manjo Janar Waidi Shaibu na daga cikin sababbin hafsoshin tsaron da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a makon da ya gabata.
Me ya ce kan 'yan ta'addan Lakurawa?
A yayin tantancewar, ya yi bayani kan kwarewarsa a harkar soja da kuma dabarun da yake shirin amfani da su wajen dawo da tsaro a kasar nan .
"Sojojin kasa za su ragargaji kungiyar ‘yan ta’addan da ake kira Lakurawa."
“Ana bukatar haɗin kai daga kowane ɓangare na al’umma. Tsaro ba abu ne mai arha ba, amma za mu tabbatar da yin amfani da dukkan albarkatun da ake da su ta hanyar da ta dace."
- Manjo Janar Waidi Shaibu
Janar ɗin ya tabbatar wa ‘yan majalisar cewa karkashin jagorancinsa, rundunar za ta kara kaimi wajen kai hare-hare kan ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.
Manjo Janar Shaibu ya fadi kwarewarsa
A lokacin da yake tuna gogewarsa a filin daga, Shaibu ya ce ya taka muhimmiyar rawa a yaki da Boko Haram a jihar Borno, inda aka samu gagarumar nasara a lokacinsa, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar da labarin.
“Mun samu nasara kan Boko Haram a shekarar 2015, kuma da yawa daga cikin ‘yan ta’addan sun mika wuya a lokacin da nake aiki."
“Mun yi amfani da fasahar zamani wajen inganta ayyukan tsaro, kuma a cikin shekaru biyar da suka gabata, na taka muhimmiyar rawa a hare-haren da suka rage karfin ‘yan ta’adda sosai.”
- Manjo Janar Shaibu

Source: Twitter
Manjo Janar Shaibu ya kuma jaddada muhimmancin kulawa da jin daɗin sojoji da cigaban aikinsu, yana mai cewa waɗannan abubuwan za su taka muhimmiyar rawa wajen jagorancinsa a rundunar sojoji.
Zaman tantancewar ya ƙare ne bayan ‘yan majalisar sun yaba da tarihin aikinsa tare da umartarsa da ya yi gaisuwa ya tafi, alamar amincewa da nadinsa.
Muna yi masa fatan alheri
Ibrahim Kabir ya shaidawa Legit Hausa cewa alkawarin da sabon hafsan sojojin kasan ya dauka abin a yaba ne.
"Ya nuna bada wasa ya zo ba kuma muna yi masa fatan samun nasarar cika wannan alwashin da ya dauka."
"Matsalar rashin tsaro ta addabi mutanen Najeriya, muna fatan Allah ya kawo mana karshenta."

Kara karanta wannan
Bayan Tinubu ya naɗa sababbin hafsoshin tsaro, an canjawa Janar sama da 60 wurin aiki
- Ibrahim Kabir
Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara kan 'yan bindiga masu dauke da makamai a jihar Kebbi.
Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga sama da 80 bayan sun yi artabu da su lokacin da suka yi yunkurin shigowa Kebbi daga jihar Zamfara.
Hakazalika, dakarun sojojin kwato babura masu yawa tare da kubutar da mutanen da 'yan bindigan suka yi garkuwa da su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

