Pantami Ya Magantu kan Hana Wa’azi, Ya Tabo Batun Malamai da Ke Sukar Juna

Pantami Ya Magantu kan Hana Wa’azi, Ya Tabo Batun Malamai da Ke Sukar Juna

  • Sheikh Isa Ali Pantami ya yi magana kan hana wa’azi kai tsaye da wasu ke ganin hakan zai kawo daidaito a cikin al'umma
  • Ya ce kungiyoyin kamar JNI, Izalah, Tijjaniyya da Kadiriyya ya dace su jagoranci tsara dokoki da kula da masu wa’azi
  • Pantami ya kuma gargadi malamai su guji sukar junansu a bainar jama’a, yana cewa kafofin sadarwa sun haifar da yawaitar jayayya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Wasu al'umma da dama na kiran a samar da ka'ida ko kuma sanya doka kan malaman addini da ke gudanar da wa'azi.

Sheikh Isa Pantami ya yi magana kan lamarin inda ya bayyana matsayarsa kan hana wa'azi da sanya ka'idoji.

Pantami ya fadi matsayarsa kan hana wa'azi a Najeriya
Tsohon minista a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami. Hoto: Prof. Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Pantami ya bayyana haka ne a cikin wani faifain bidiyo da DW Hausa ta wallafa a Facebook a yau Laraba 29 ga watan Otobar 2025.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga saman babura sun kai hari a Kano, an yi barna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Pantami ya yi bayani kan hana wa'azi

A bidiyon, malamin ya ba da shawara, ya ce bai goyon bayan hana wa'azi kai tsaye inda ya kawo tsare-tsaren da ya kamata a bi.

Ya ce:

"Ni ba na goyon bayan gwamnati kai tsaye ta dauki mataki na bada damar yin wa'azi ko hanawa, tsarin da nake tunani shi ne samar da tsari a kowane jiha na kungiyoyi.
"Kungiyoyin su kunshi wakilci na JNI da Izalah, Tijjaniya da Kadiriyya da Musulmai lauyoyi da duk wadanda suka dace.
"Su rika ba da ka'aidoji da Musulmai, su za su yi dokar, ya zamto daga matakin jiha karkashin Sultan su rika kula da masu wa'azi, wani ana yi masa gargadi wani kuma kashedi ko kuma dakatar da shi."
Pantami ya ba malamai kan sukar juna yayin wa'azi
Farfesa Isa Ali Pantami a cikin ofishinsa. Hoto: Prof. Isa Ali Pantami.
Source: UGC

Pantami ya shawarci malamai kan sukar juna

Har ila yau, Pantami ya yi tsokaci kan yadda malamai ke sukar junansu inda ya ce abin takaici ne kuma ba haka ya dace ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Mutfwang ya fadi matsayarsa bayan fuskantar matsin lambar ya koma APC

Pantami ya ce ya kamata masu koyarwa su ji tsoron Allah duba da yadda yanzu kafofin sadarwa suka ba mutane dama tsoma baki a lamuran addini.

"Wani malami a Najeriya ya ce masu ilimi su daina yin jayayya a bainar jama'a ka da jahilai su fara saka baki, abin takaici yanzu kafofin sadarwa sun sa kowa ya zama mai musu da jayayya.
"Wanda yake da ilimi da wanda bai da ilimi su yi ta tsoma baki, masu karantarwa mu yi koyarwa tsakaninmu da Allah, a bangarori da dama da ake samun matsala kashi 90 an yi tarayya a kai, kadan ne ake da matsala.
"A yanzu wadanda suke tare a kan komai ma daga daya daga cikinsu ya yi kuskure sai a fara tozarta shi, mu rika kyautatawa juna lafazi da kuma zato."

- Sheikh Isa Ali Pantami

Sheikh Pantami ya ce idan mutum ya yi maka ba daidai ba, ka kira shi a waya ka ce wane na ji an ce kaza, watakila idan ka gamsar da shi zai fito har yi maka godiya.

Hakimin Pantami ya yabawa Farfesa Isa Ali

Kara karanta wannan

'Ka da ku biya kuɗin fansa': Gargaɗin Malami idan ƴan bindiga suka sace shi

Kun ji cewa masarautar Pantami ta karrama Sheikh Isah Ali Pantami bisa irin gudunmawar da yake bayarwa ga al'umma.

Hakimin Pantami ya yaba da ayyukansa a bangaren lafiya, ilimi, tsaro da kuma kyautata rayuwa.

‘Yan Najeriya da dama a kafafen sada zumunta sun taya shi murna, tare da yi wa malamin fatan alheri.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.