Yadda Rufe Matatar Fatakwal Ya Kassara Tattalin Arziki, An Yi Asarar N366.2bn
- Wani rahoto ya bankado cewa Najeriya ta tafka gagarumar asara sakamakon rufe matatar mai da ke Fatakwal a jihar Ribas
- An gano cewa gwamnati yi asarar fiye da Dala miliyan 249.7, kimanin Naira biliyan 366.2 kenan, cikin watanni biyar kacal
- Rahotanni sun bayyana cewa matatar ba ta taba tace mai yadda ya kamata tun bayan sake bude ta a Nuwamba 2024 ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers – Gwamnatin Najeriya ta yi babbar asara bayan rufe matatar man Fatakwal wacce ita ce babbar matatar mai a kasar.
Rahotanni sun ce matakin ya jawo wa gwamnati asarar da ta kai Naira biliyan 366.210 a cikin kwanaki 156, daga 24 ga Mayu zuwa 31 ga Oktoba 2025.

Source: Twitter
Binciken Daily Trust ya gano cewa an samu asarar ne bayan an dakatar da aiki a wurin watanni biyar da suka gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ta kashewa matatar mai kudi
Rahoton ya ce matatar da ke Eleme, Jihar Ribas, ta fara aiki a Nuwamba 2024 bayan gwamnati ta kashe Dala biliyan 1.5 don gyaran ta gaba ɗaya.
Kamfanin mai na NNPCL ta bayyana a lokacin cewa a wancan lokaci, tana da karfin tace ganguna 60,000 a rana.
Haka kuma tana samar da lita miliyan 1.4 na man fetur, lita 900,000 na kalanzir, da lita miliyan 1.5 na dizal a kullum.

Source: Twitter
Sai dai a watan Mayu 2025 an rufe ta saboda abin da NNPCL ta kira wani gyara da kamfanin man ya ce za a yi.
Wannan mataki ya haifar da asarar da aka kiyasta ya kai akalla Dala miliyan 249.7 a cikin watanni biyar kacal.
Idan aka lissafa farashin man fetur da ke kusan ₦900 a lita, da sauran nau’o’in man da matatar ke tacewa, jimillar kudin da gwamnati ta rasa ya kai akalla Naira biliyan 366.2.
Ma'aikatan matatar mai sun yi fallasa
Wasu ma’aikatan matatar sun ce matatar bata taba tace mai a zahiri ba tun bayan sake budeta a 2024, duk da ana fitar da tataccen mai daga cikinta.
Sun ce man da ake cewa “an tace” ana shigo da shi ne daga wasu wurare, ana shiryawa a cikin matatar sannan a fitar da shi ga ‘yan kasuwa.
Wata majiya da ta nemi a sakaye sunanta ta ce:
“Sun hana mu magana da ‘yan jarida. Amma gaskiya ita ce, ba a taba tace mai a nan ba tun Nuwamba 2024. Man da ake fitarwa ana kawo shi ne ta kamfanin Indorama, su tsaftace shi, sai a ce matatar Fatakwal ce ta tace.”
Shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari, ya amince da cewa matatar tana da matsaloli masu yawa wanda sakaci na shekaru da dama.
Ya ce kafin a dakatar da aiki, NNPCL na asara tsakanin N300m zuwa N500m a wata saboda rashin ingancin tsarin tace mai.
Majalisa ta fara binciken matatun mai
A wani labarin, mun wallafa cewa majalisar wakilai ta Najeriya ta dauki matakin bincike kan yadda aka kashe Dala biliyan 18 wajen gyaran manyan matatun mai da gwamnati ke da su.
'Dan majalisa, Hon. Sesi Oluwaseun Whingan ya ce ko da an kashe wannan kudi mai yawa, har yanzu babu wani katabus da ake iya yi na tace mai a matatun Fatakwal, Kaduna da Warri.
'Yan majalisar sun kafa kwamiti da zai yi bincike mai zurfi a kan yadda aka kashe makudan Dalolin da zummar gano yadda ake samun matsala wajen farfado da matatun su fara aiki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


