2027: Gwamnonin Arewa 3 na tsaka Mai Wuya game da Barin PDP zuwa APC
- An samu bayanai cewa wasu daga cikin gwamnonin PDP a Arewacin Najeriya na tsaka mai wuya a jam'iyyar adawar
- Majiyoyi sun nuna PDP na fuskantar rikici yayin da gwamnoni ke shirin komawa APC, abin da wasu ke ganin baraza ne
- APC ta tabbatar da cewa gwamnoni hudu a Najeriya na cikin tattaunawar komawa jam’iyyar, kafin ƙarshen shekarar bana
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Matsaloli na ƙaruwa a siyasar Najeriya yayin da ake ganin ƙasar na iya gangarawa zuwa tsarin jam’iyya ɗaya.
Majiyoyi sun ce jam’iyyar PDP ta fara rasa gwamnoni da mambobi masu ƙarfi zuwa APC mai mulki.

Source: Facebook
Jaridar The PUNCH ta ruwaito cewa gwamnoni uku daga yankin Arewa na jam’iyyar PDP na shirin sauya sheƙa zuwa APC kafin zaɓen 2027, abin da ya jefa jam’iyyar cikin rudani da raunin tsari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Halin da jam'iyyar PDP ta shiga a yanzu
Jam'iyyar PDP, wadda ta yi mulki tsawon shekaru 16 bayan komawar Najeriya ga dimokuraɗiyya a 1999, yanzu tana mulkin jihohi takwas kacal daga cikin 36.
Jihohin sun hada da Bauchi, Oyo, Adamawa, Osun, Plateau, Taraba, Zamfara da Rivers, wannan shi ne mafi rauni da jam’iyyar ta taba shiga a tarihinta.
Rahotanni sun ce bayan sauya shekar wasu gwamnoni kamar Sheriff Oborevwori na Delta, Umo Eno na Akwa Ibom da Peter Mbah na Enugu, yanzu hankula sun koma kan jihohin Plateau, Taraba, Zamfara da Adamawa.
Hasashe daga Taraba, Adamawa da Plateau
A Taraba, wasu majiyoyi sun tabbatar cewa Gwamna Agbu Kefas na iya barin PDP nan ba da daɗewa ba domin komawa APC, abin da zai kawo ƙarshen mulkin PDP da ya daɗe har shekaru 26 a jihar.
“Ba jita-jita ba ce, tattaunawa ta kai mataki mai zurfi.”
- Cewar wani hadimin gwamnan
A Adamawa kuwa, ana zargin Gwamna Ahmadu Fintiri yana cikin tattaunawa da APC, kodayake hadimansa sun musanta, suna cewa yana da niyyar ci gaba da kasancewa cikin PDP.
Sai dai wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa gwamnoni da dama na amfani da tattaunawar a matsayin hanyar neman kusanci da gwamnatin tarayya, cewar Vanguard.

Source: Twitter
Martanin gwamna kan matsin lamba daga APC
A Plateau, Gwamna Caleb Mutfwang ya tabbatar cewa akwai matsin lamba daga APC da wasu manyan jiga-jigai a fadar shugaban kasa don ya sauya sheƙa.
Amma Caleb Mutfwang ya ce ba zai bar PDP ba sai idan Allah da jama’an da suka zaɓe shi sun umarce ya yi hakan.
Sai dai wani rukuni na APC a yankin Arewa ta Tsakiya ya nuna goyon bayansu ga shigar Mutfwang jam’iyyar, suna zargin wasu shugabannin da suka yi watsi da shi da son kai.
APC ta ce ta buɗe ƙofofinta ga duk wani ɗan siyasa mai nagarta da ke son haɗa kai da gwamnatin Tinubu, tare da bayyana cewa waɗannan sauye-sauye za su ƙara ƙarfafa jam’iyyar.
APC ta shawarci 'yan kasa kan wahalhalu
Kun ji cewa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya shawarci ‘yan Najeriya su riƙa tuhumar gwamnonin jihohi.
Shugaban kam'iyyar ya ce kowanne gwamna yanzu yana karɓar fiye da ninki uku na abin da ake ba su a baya saboda ƙarin kuɗin da aka samu.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tana kan hanya madaidaiciya wajen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


