Aiki ga Mai Kare Ka: Badaru Ya Gana da Hafsoshin Tsaro, Ya Ja Kunnensu
- Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya gana da sabbabbin hafsoshin tsaro da Shugaba Bola Tinubu ya nada
- Badaru ya bukace su da su haɗa kai da juna wajen tabbatar da zaman lafiya a ƙasar da kuma kare dukiyoyin al'umma
- Ya ce shugabancin Tinubu na sa ran ganin sakamako mai gamsarwa da kuma ingantaccen haɗin kai tsakanin rundunonin tsaron Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya yi wata ganawa ta musamman da sababbin hafsoshin tsaro a Najeriya.
Badaru ya bukaci sababbin shugabannin rundunonin tsaro da su ƙara haɗin kai da samar da sakamako wajen yaki da rashin tsaro.

Source: Facebook
Badaru ya gana da hafsoshin tsaron Najeriya
Badaru ya yi wannan kira ne yayin da manyan hafsoshin tsaro suka kai masa ziyara a Abuja, kamar yadda hadiminsa a bangaren sadarwa, Mati Ali ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda suka ziyarce shi sun haɗa da Babban Hafsan Tsaro, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, da Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Manjo Janar Waidi Shaibu.
Sauran sun haɗa da Babban Hafsan Sojin Ruwa, Real Admiral Idi Abbas, da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Vice Marshal S.K. Aneke.
A cikin sanarwar da Mati ya fitar, ya ce Badaru ya taya su murna bisa nadin da Shugaba Tinubu ya yi musu.
Ya bayyana cewa nadin nasu alama ce ta jajircewar shugaban ƙasa wajen ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa da gyaran rundunonin sojoji.
“Lokacin nadin ku ya zo ne da ƙasa ke buƙatar shugabanci na haɗin kai da tsari. Shugaban ƙasa ya nuna cikakken amincewa da ku.”
- Badaru Abubakar
Ya ce wajibi ne yanzu su yi amfani da wannan amincewa zuwa aikace-aikacen da za su samar da nasarori a filin yaki.
Ministan ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin rundunonin tsaro, musamman wajen tsara haɗaɗɗun ayyuka da musayar bayanan leƙen asiri.
Ya ce hakan zai taimaka wajen magance barazanar tsaro da ke fitowa daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Source: Facebook
Albishiri da Badaru ya yi wa hafsoshin tsaro
Badaru ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa za ta ci gaba da bayar da jagoranci da kulawa ga rundunonin tsaro a dukkan matakai.
Ya ƙara da cewa za su tallafa musu da kayan aiki da shawarwari domin tabbatar da tsaro da daidaito a fadin ƙasa.
Taron ya samu halartar manyan jami’ai daga Ma’aikatar Tsaro da manyan hafsoshin hedkwatar rundunonin tsaro.
Badaru ya bayyana tabbacin cewa ƙarƙashin sabon shugabancinsu, sojojin Najeriya za su ƙara inganta kwarewa da amincewar jama’a a aikinsu.
Ya kuma ce gwamnati na sa ran ganin sababbin shugabannin tsaro sun tabbatar da daidaito, kwanciyar hankali da zaman lafiya a ƙasar baki ɗaya.
Za a tantance sababbin hafsoshin tsaro
Mun ba ku labarin cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya mika sunayen sababbin hafsoshin tsaro ga majalisar dattawa domin tantance su.
Tinubu ya bukaci majalisar da ta gaggauta amincewa da nadin da ya yi wa sababbin hafsoshin a matsayin wadanda za su jagoranci rundunonin tsaro.
Bayan karbar bukatar, majalisar dattawa ta sanya lokacin da za ta tantance su don duba yiwuwar amincewa da nadin da aka yi musu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


