NDLEA: Abba Kyari Ya Samu Tangarda da Kotu Ta Yi Watsi da Buƙatarsa
- Kotu ta kori bukatar Abba Kyari da sauran wadanda ke neman a soke tuhumar da ake yi masu na ɓoye wasu kadarori da ake zargin nasu ne
- Alkalin kotun ya ce hukumar NDLEA ta gabatar da isassun hujjoji da ke bukatar su kare kansu daga tuhumar da ake yi masu
- Kotun ta umarci jami'in 'dan sandan da wadanda ake kafa da su su fara shirin kare kansu kafin ranar 4 zuwa 6 ga Nuwamba, 2025
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja – Kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da buƙatar da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar, DCP Abba Kyari ya shigar gabanta.
Abba Kyari da wasu mutane biyu sun shigar da kara inda suka neman kotu ta soke shari’ar da hukumar NDLEA ta kai musu kan rashin bayyana kadarorinsu.

Source: Facebook
Daily Nigerian ta wallafa cewa Alkalin kotun, Mai Shari’a James Omotosho, ya ce hukumar NDLEA ta gabatar da hujjojin da suka isa don tilasta masu kare kansu.
Kotu ta yi watsi da bukatar Abba Kyari
Alkalin ya bayyana cewa kotu ba ta tabbatar da cewa suna da laifi ba tukuna, amma dole ne su bayyana hujjojin da ke hannunsu domin a yi adalci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai Shari’a James Omotosho ya ce:
“Ina ganin dukkanin shaidu da hujjojin da masu shigar da kara suka gabatar, akwai abin da ya wajabta waɗannan mutane su yi bayani."
"Wannan ba yana nufin an same su da laifi, sai dai domin a ba su damar kare kansu yadda doka ta tanada."
Abba Kyari: NDLEA ta kai shaidu kotu
Hukumar NDLEA ta shigar da tuhuma mai ɗauke da laifuffuka 23 a kan Abba Kyari da ‘yan uwansa, Mohammed Kyari da Ali Kyari.
Hukumar yaƙi da fataucin miyagun kwayoyi ta ce sun gaza bayyana duk kadarorinsu. Hakanan ta zarge su da boye dukiyar suka mallama da karkatar da kuɗi.
Hukumar ta ce waɗannan laifuffuka sun sabawa sashen 35(3)(a) na dokar NDLEA da kuma sashen 15(3)(a) na dokar hana zamba ta 2011.
A yayin shari’ar, NDLEA ta kammala gabatar da shaidu 10 tare da hujjoji akalla guda 20 a kan tuhume-tubumen kamar yadda aka gani a The Nation.

Source: Twitter
Bayan kammala gabatar da shaidun, lauyoyin Kyari suka nemi kotu ta soke shari’ar bisa hujjar cewa babu wata shaida da ke nuna sun mallaki kadarorin da ake magana a kai.
Sun ce a bisa doka, dole ne takardun mallaka na ƙasa su kasance takardu na asali da aka tabbatar kafin su zama hujja a kotu.
Sai dai Mai Shari’a Omotosho ya ce ya ƙi karɓar roƙon su na cewa babu dalilin shari’a, inda ya umarce su da su gabatar da kariyarsu daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Nuwamba.
An rokawa Kyari alfarma a wurin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Duniya (IHRC), reshen Najeriya, ta aika buƙata ta musamman ga Shugaba Bola Tinubu da ya yi afuwa ga DCP Abba Kyari.
Wannan roƙon, wanda aka fitar ta hannun Dr. Duru Hezekiah, shugaban IHRC a Najeriya, ya ƙunshi buƙatar tattaunawa ta ƙasa don a duba yiwuwar yi wa Kyari afuwa bisa dokar kasa.
IHRC ta bayyana cewa bukatar afuwar ba tana nufin a yafe laifi ba, amma tana iya zama wata dama ta amfani da ƙwarewar Abba Kyari wajen taimaka wa ƙasa idan aka ga ya cancanta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


