Akwai Matsala: 'Yan Ta'adda da Masu Zanga Zanga Sun Yi Barazanar Kai Hari Majalisar Tarayya
- 'Dan Majalisar Wakiali, Honarabul Garba Ibrahim Muhammad ya koka kan halin matsalar tsaron da suke fuskantar a wajen aikinsu
- Shugaban kwamitin tsaron cikin gida ya yi ikirarin cewa yan ta'adda da masu zanga zanga sun yi barazanar kai hari zauren Majalisa
- Ya ce akwai bukatar samar tsaro a Majalisa domin kare mambobi daga barazanar da suke fuskanta daga bangarori daban-daban
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeriya – Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Tsaron Cikin Gida, Hon. Garba Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa sun samu sakon barazanar hare-hare daga ‘yan ta’adda da masu zanga-zanga.
Hon. Garba Ibrahim ya yi ikirarin cewa 'yan ta'adda da wasu masu zanga-zanga sun yi barazanar ƙona ginin Majalisar Dokoki ta Tarayya ko kuma rufe ta baki ɗaya.

Source: Facebook
Matsalolin tsaron da ake fuskanta a Majalisa
Ya ce Majalisar Tarayya na fuskantar manyan matsalolin tsaro, ciki har da satar motoci da babura, lalata kayan gwamnati da ƙirƙirar takardun shaida na karya, in ji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan Majalisar ya fadi hakan ne a ranar Talata yayin taron jin ra’ayoyin jama’a kan kudirin dokar da ke neman kafa Hukumar Tsaron Majalisa, wanda ya gudana a Abuja.
Kudirin ya kunshi kafa tsari na musamman don horar da jami’an tsaro na majalisa da tabbatar da tsaro ga ‘yan majalisa, ma’aikata da baƙi.
Ya ce ‘yan majalisa na fuskantar barazana kai tsaye daga wasu ‘yan mazabunsu da ke samun damar shiga ofisoshinsu ba tare da izini ko tanadi ba.
An yi barazanar kai hari Majalisar Tarayya
Ya kuma gargadi cewa idan ba a ɗauki matakan tsaro cikin gaggawa ba, hakan na iya katse ayyukan majalisar gaba ɗaya, ciki har da wakilci, binciken gwamnati, da tattaunawar kasafin kuɗi.
"Majalisar Tarayya na fama da matsalolin tsaro da dama. Mun fuskanci satar motoci, lalata kayan gwamnati, amfani da katin shaida na bogi, shigowar baki cikin majalisa ba tare da takardun izini ba.
“Mun sami barazanar daga ‘yan ta’adda cewa za su tashi bam a ginin Majalisar Dokoki, da kuma masu zanga-zanga da ke barazanar rufeta.
"‘Yan majalisa na fuskantar barazana daga wasu daga cikin jama'an mazabunsu da ke shigowa ofisoshinsu ba tare da izini ba.”
- Hon. Garba Ibrahim Muhammad.

Source: Facebook
Hon. Garba ya ce wadannan kalubalen tsaro na iya kawo cikas ga tsarin mulki da gudanar da majalisa, yana mai cewa kudirin da ake tattaunawa zai kawo karshen matsalar ta hanyar bin tsarin tsaro na duniya, in ji The Nation.
Tinubu ya aika wasika Majalisar Dattawa
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika sunayen sababbin hafsoshin tsaron da ya nada zuwa Majalisar Dattawa.
A wasikar da ya tura ranar Talata, Bola Tinubu ya bukaci sanatoci su hanzarta tantancewa da tabbatar da nadinsu domin su kama aiki kan tsarin tsaron kasar nan.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasikar shugaban ƙasa a zamansu na ranar Talata, 28 ga watan Oktoba, 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


