Bayan Karbar Bukatar Tinubu, Majalisa Ta Sa Lokacin Tantance Sababbin Hafsoshin Tsaro
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika sunayen sababbin hafsoshin tsaro ga majalisar dattawa domin tantancewa da tabbatar da su
- Mai girma Bola Tinubu ya bukaci majalisar da ta gaggawar amincewa da nadin da ya yi wa sababbin hafsoshin a matsayin wadanda za su jagoranci rundunonin tsaro
- Bayan karbar bukatar shugaban kasan, majalisar dattawa ta sanya lokacin da za ta tantance su don duba yiwuwar amincewa da nadin da aka yi musu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta cin ma matsaya kan lokacin tantance sababbin hafsoshin tsaro da Shugaba Bola Tinubu ya nada.
Majalisar dattawan ta matso da ranar da za ta gudanar da tantance sababbin hafsoshin tsaro zuwa Laraba, 29 ga Oktoba, maimakon mako mai zuwa kamar yadda ta tsara a baya.

Source: Twitter
Tashar Channels tv ta kawo rahoto cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana hakan a ranar Talata, 27 ga watan Oktoban 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar dattawa ta samu wasikar Tinubu
Sanarwar ta fito ne bayan Godswill Akpabio, ya karanta wata wasika daga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
A cikin wasikar, Shugaba Tinubu ya nemi majalisar ta tabbatar da nadin sabon babban hafsan tsaron kasa (CDS), Janar Olufemi Oluyede da sauran hafsoshin tsaro.
Akpabio ya bayyana cewa canjin ranar ya zama wajibi ne domin bai wa sababbin hafsoshin tsaron damar fara aiki ba tare da bata lokaci ba.
Shugaba Tinubu ya roki majalisar dattawa da ta yi gaggawar tabbatar da nadin domin tabbatar da ci gaba da daidaito a tsarin tsaro na kasar nan.
Yaushe za a tantance hafsoshin tsaro?
Jaridar The Punch ta ce a cewar sabon jadawalin, babban kwamitin majalisar zai gudanar da tantancewar a ranar Laraba, 28 ga watan Oktoban 2025.
Wannan ci gaban ya zo ne kwana biyu bayan ganawar sirri da Shugaba Tinubu ya yi da sababbin hafsoshin tsaro a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.
Ganawar dai ita ce ta farko tun bayan sauya manyan hafsoshin tsaron da Shugaba Tinubu ya yi.

Source: Facebook
Tinubu ya sauya hafsoshin tsaro
A cikin sauyin, Tinubu ya sauke Janar Christopher Musa daga matsayin babban hafsan tsaro, tare da mayar da Janar Olufemi Oluyede, tsohon hafsan sojoji kasa, a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
Sai dai ya bar Manjo Janar E.A.P. Undiendeye a matsayin hafsan rundunar leken asiri ta kasa.
Shugaban kasa ya bukaci sababbin hafsoshin da su nuna bajinta, kishin kasa, da hadin kai a cikin rundunonin sojoji.
Tinubu ya samu yabon nada hafsoshin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya kwararo yabo ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan nada sababbin hafsoshin tsaro.
Gwamna Ododo ya yabawa shugaban kasan musamman kan nada Manjo Janar Waidi Shaibu, dan asalin jihar Kogi a matsayin hafsan sojojin kasan Najeriya.
Hakazalika, Gwamna Ododo ya ce samun ɗan asalin Kogi a irin wannan matsayi babban abin alfahari ne ga mutanen jihar, inda ya jaddada cewa kwalliya za ta biya kudin sabulu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

