Sheikh Musal 'Kasiyuni Ya Yi Kalamai Masu Zafi, Ya Zargi Gwamnatin Kano da Nuna Wariya

Sheikh Musal 'Kasiyuni Ya Yi Kalamai Masu Zafi, Ya Zargi Gwamnatin Kano da Nuna Wariya

  • Sheikh Musal ‘Kasiyuni Sheikh Nasiru Kabara ya soki gwamnatin jihar Kano bisa yadda ta rarraba mukamai tsakanin mabiya dariku daban-daban
  • Malamin ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da nuna wariya ga mabiya Muhammadiyya duk da gudunmawar da suka bayar a zaben da ya gabata
  • Ya kuma gargadi malaman da ke wajen Kano da su daina tsoma baki a cikin al’amuran addini da na siyasar jihar, ganin yadda ba su da ruwa a ciki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Malamin addinin Musulunci, Sheikh Musal ‘Kasiyuni Sheikh Nasiru Kabara, ya bayyana fushinsa kan yadda gwamnatin jihar Kano ke rarraba mukamai cikin bangaranci.

A cewar sa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi watsi da mabiya Muhammadiyya, duk da cewa sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar gwamnatinsa a zaben da ya gabata.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya yi bayani a kan hakkin matan da mazansu ke gallazawa azaba

Sheikh Musal 'Kasiyuni ya dura a kan gwamnatin Kano
Taswirar jihar Kano, inda ake takaddama a kan bambancin darika Hoto: Legit.ng
Source: Original

A wani karatun da Salihu Mu’az Koki ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh ‘Kasiyuni ya zargi gwamnatin Kano da mayar da su “bare” a jiharsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musal Kasiyuni ya fusata da gwamnatin Kano

Malamin ya ce, a ma’aikatun addini da ke Kano, babu wanda aka bai wa jagoranci daga cikin mabiya Bakadire, sai dai a ce an ba su ga mabiya Wahabiyya.

A cewarsa:

“Duk ma’aikatun addini a garin nan, sai suka damkawa Wahabiyawa. Kuma a cikin Wahabiyawan ma aka zabi wani da ya shafe kusan shekaru goma yana jagoranta, aka sake damka masa, sai ka ce gadon ubansa ne.”

Sheikh ‘Kasiyuni ya ce gwamnatin Kano ta yi biris da wadanda suka yi mata aiki, kuma har yanzu ta ki ta waiwaye su da mukaman da suka dace.

Batun hukumar Hisbah da Abdul Jabbar Kabara

Bisa dukkan alamu malamin ya tabo zancen hukumar Hisbah wanda Abba Kabir Yusuf ya sake damka ta a hannun Sheikh Aminu Daurawa a 2023.

Kara karanta wannan

Sanata Ned Nwoko ya fadi abubuwa 2 da za su dawo da zaman lafiya Kudu maso Gabas

Shehin Kadiriyyan ya nuna 'yan Izala ne kurum su ke shugabantar hukumar duk da an samu irinsu Sheikh Mu'azzam Mai Bushra da Yahaya Faruk Chedi.

Bayan haka, ya yi wa mabiyansa albishir da labari mai dadi game da Abdul Jabbar Kabara wanda aka dauke daga gidan maza a Kano zuwa Abuja.

Sheikh ‘Kasiyuni ya dura kan gwamnati

Malamin ya kara bayyana cewa gwamnatin Kano ta nuna son kai, inda ta fifita mabiya Wahabiyya fiye da sauran kungiyoyin addini.

A cewarsa:

“A jiharmu yanzu mun zama ‘yan bora, ita kuma Wahabiyya ta zama ‘yan mowa. Ta ya ba za su mike kafarsu a Kano ba? Ta ya ba za su yi shegantaka da fitsara ba?”
Sheikh Musal 'Kasiyuni ya soki gwamnatin Kano
Hoton Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ya kuma caccaki malaman da ke wajen Kano amma ke tsoma baki cikin harkokin addini da sauran al'amuran jihar.

Sheikh ‘Kasiyuni ya ce:

“In za ka yi magana, yi magana a garinka. Ba ka da hakki a cikin Kano. Wani abu yana faruwa a wata jiha, sai wani daga waje ya sa baki? Wannan raini ne.”

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi ya yi wa masu suka martani kan nada dan uwansa sarki

Sheikh ‘Kasiyuni ya gargadi wadannan malamai da su daina tsoma baki cikin al’amuran da suka shafi Kanawa.

Sheikh Dahiru Bauchi ya godewa Shugaban Aljeriya

A baya, mun wallafa cewa fitaccen malamin addinin Musulunci daga jihar Bauchi, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi godiya ga shugaban ƙasar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune.

Ya mika godiyarsa bayan Shugaban Kasan ya bayar da guraben karatu ga wasu daga cikin almajiran Sheikh Dahiru Bauchi ta hannun gidauniyar fitaccen malamin.

Malamin ya bayyana cewa wannan taimakon ya wuce kasancewa damammaki na karatu kadai, yana mai cewa hakan na ƙarfafa alaƙar ƙasashen Musulmai da musayar ilimi da fahimta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng