Sheikh Gumi Ya Yi Bayani a kan Hakkin Matan da Mazansu ke Gallazawa Azaba

Sheikh Gumi Ya Yi Bayani a kan Hakkin Matan da Mazansu ke Gallazawa Azaba

  • Sheikh Ahmad Gumi ya bukaci alƙalai da malamai su kare hakkin mata masu fama da cin zarafi a gidajen aurensu
  • Malamin ya ce addinin Musulunci bai amince da zalunci ba, kuma yana bai wa maza da mata damar rabuwa idan soyayya ta kare
  • Ya yi kira ga alƙalai su yi adalci su kuma tsaya da gaskiya wajen warware matsalolin auratayyar don kawar da zalunci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci alƙalan Musulunci da sauran malamai a kan lamarin matan da ke cikin wahala a gidajen aurensu.

Sheikh Gumi ya shawarce su da su tabbatar cewa mata masu fama da zalunci a gidajen aure sun samu ‘yancin neman saki daga mazajensu.

Kara karanta wannan

Sanata Ned Nwoko ya fadi abubuwa 2 da za su dawo da zaman lafiya Kudu maso Gabas

Sheikh Gumi ya ce babu zalunci a Musulunci
Sheikh Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin musulunci Hoto: Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa malamin ya yi wannan kira ne a tafsirin mako-mako da yake gudanarwa a masallacin Sultan Bello, Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Gumi ya shawarci alkalan musulunci

Sheikh Gumi ya shawarci alkalai da su raba auren da ake zaluntar matar ba tare da an nemi ta biya diyya ba.

Malamin ya jingina bayaninsa da littafin Al-Mukhtasar Al-Khalil, wani muhimmin littafi na fikihu na mazhabar Malikiyya.

Ya jaddada cewa Musulunci bai yarda da zalunci a aure ba, kuma Allah ya ba kowane bangare damar kawo ƙarshen aure idan lamari ya dagule.

Sheikh Gumi ya shawarci alkalai su kare hakkin matan da ake zalunta
Hoton fitaccen Malami, Sheikh Gumi Hoto: Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Gumi ya nuna damuwa kan yadda wasu dokoki da al’adu ke fifita maza wajen neman saki, amma suna kafa cikas ga matan da ake wulakantawa a auren.

Sheikh Gumi ya ce:

“Namiji zai iya cewa kalma ɗaya kawai ya rabu da matarsa, amma idan mace ta nemi ‘yanci daga mijin da ke zaluntar ta, sai a ƙara mata azaba ta hanyar cewa sai ta biya diyya. Wannan zalunci ne, kuma Musulunci ya haramta zalunci.”

Kara karanta wannan

Fasahar AI za ta kawo matsala a ayyukan mutane? Sheikh Isa Pantami ya yi bayani

Ya ambaci ayoyin Alƙur’ani (Suratu Nisa’i: 35, 19, da 130), yana mai cewa Allah Ya halatta rabuwa idan zaman lafiya ya gagara, tare da tabbatar da adalci ga ɓangarorin biyu.

Sheikh Ahmad Gumi ya fusata

Malamin ya yi tir da yadda ake samun karuwar tashin hankali a cikin aure, inda wasu maza ke cin zarafin matansu ta hanyoyi daban-daban, sannan su ki sakinsu sai an biya diyya.

Gumi ya ce idan mijin ya zaga, wulakanta ko ya doke matarsa, to ya rasa hakkin neman diyya ta tsarin da musulunci ya amince mace ta nemi rabuwar aure, wato Khul'i.

Ya kuma yi kira ga alƙalan Musulunci su kasance masu jarumta da gaskiya wajen yanke hukunci domin kare mata daga zalunci.

Sheikh Gumi ya jaddada cewa aure mai kyau a Musulunci yana ginuwa ne kan tausayawa, jinƙai, da mutunta juna, amma akasin hakan na iya jawo rabuwar auren.

Shawarar Gumi ga gwamnatin Kano

A baya, mun wallafa cewa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya bukaci gwamnatin Kano ta kawo karshen haniyar addini a jihar.

Kara karanta wannan

Sauya kundin mulki: Majalisa ta fara bitar bukatun kirkirar jihohi 55 a Najeriya

Sheikh Gumi ya yi wannan kira ne a karatun da ya gabatar a ranar 9 ga Oktoba, 2025, inda ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta tsaya tsayin daka wajen kare martabar addini.

A cewar sa, dole gwamnati ta tabbatar da adalci da kuma fahimtar mabiya addinin Musulunci, domin hana rikicin akida da ya fara samun tushe a tsakanin malaman Kano.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng