Bayan Dawo da Su, Dangote Ya Tura Ma'aikatan Matatarsa da ya Kora Zamfara, Borno

Bayan Dawo da Su, Dangote Ya Tura Ma'aikatan Matatarsa da ya Kora Zamfara, Borno

  • Matatar Dangote ta dawo da wasu injiniyoyi da aka kora a lokacin rikicinta da kungiyar PENGASSAN
  • Ma’aikatan sun samu takardun daukar aiki da tura su zuwa jihohin Borno, Benue, Zamfara da sauransu
  • Wasu daga cikinsu sun nuna damuwa saboda rashin cikakken adireshin wuraren aiki da kuma matsalar tsaro

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas – Bayan makonni da rikici tsakaninta da ƙungiyar ma’aikatan mai da iskar gas ta ƙasa (PENGASSAN), matatar Dangote ta dawo da wasu injiniyoyi da ta kora.

Sai dai bayan dawo da su, rahoto ya nuna cewa an sake tura su zuwa wuraren ayyuka a sassa daban-daban na ƙasar.

Alhaji Aliko Dangote
Aliko Dangote da wani sashe na matatar shi. Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

Rahoton Punch ya nuna cewa ma'aikatan sun karɓi takardun sake ɗaukar aiki daga kamfanin a ƙarƙashin wani sharadi da aka gindaya.

Kara karanta wannan

An gano daloli, motoci da alfarma da Tinubu ya ware wa korarrun hafsoshin tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa an umarci ma’aikatan su isa wuraren aikinsu cikin kwana 14, idan ba haka ba, za a soke damar aikin.

Jihohin da Dangote ya tura ma'aikata

Majiyoyi daga cikin rukunin kamfanonin Dangote sun tabbatar da cewa an tura ma’aikatan zuwa wurare kamar wajen hakar ma’adinai a jihar Benue.

Haka zalika an tura wasu wuraren ayyukan gina tituna a Borno da Ebonyi, da kuma masana’antar shinkafa a jihohin Kebbi, Niger, Sokoto da Zamfara.

Wani daga cikin ma’aikatan ya bayyana cewa:

“An sake ɗauke mu gaba ɗaya, inda kowane ɗaya zai tafi wurin da aka tura shi.”

Wasu daga cikin takardun da ke dauke da sharudan aikin sun nuna cewa za a ba ma'aikatan horo na tsawon shekara biyu a wajen hako ma'adinai da ke Okpokwu, jihar Benue.

Sharudan aiki da Dangote ya kafa musu

A cikin takardar, kamfanin ya bayyana cewa ma’aikatan za su fara horo na musamman domin samun ƙwarewa, kuma za a rika tantance ƙwarewarsu lokaci zuwa lokaci.

Kara karanta wannan

Rusau ya taɓa Musulmai: Gwamna ya rushe kasuwa, an taba masallaci a Lagos

An kuma bayyana cewa kowane bangare na iya kawo ƙarshen aikin ta hanyar sanarwa kafin wata ɗaya ko biyan albashin wata ɗaya a maimakon hakan.

Alhaji Aliko Dangote da ma'aikatansa
Attajirin Afrika, Aliko Dangote da wasu ma'aikatansa a Legas. Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Takardun sun kasance ƙarƙashin sa hannun jami'in kamfanin, Femi Adekunle, wanda ya yi maraba da su zuwa wani bangare bayan barin matatar mai.

Korafin da ma'aikatan Dangote suka yi

Wasu daga cikin ma’aikatan da suka karɓi wasiƙar sun bayyana damuwarsu kan yadda aka tura su zuwa yankunan da ake fama da rashin tsaro kamar Borno da Zamfara.

Sun ce wasikar ba ta bayyana cikakken adireshin wurin da za su je ba, kuma wasu wuraren da aka ambata ba su da ofisoshi a taswirar ƙasa.

Wani ma’aikaci ya ce:

“Idan muka karɓi wasiƙar kuma muka kasa bayyana a cikin kwanaki 14, aikinmu zai ƙare. Amma babu inda aka bayyana ofishin da za mu kai rahoto,”

Sun kara da cewa shugabancin PENGASSAN ya shawarce su da kada su karɓi wasikun har sai an kammala tattaunawa da kamfanin.

Aliko Dangote zai fadada matatarsa

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin fadada matatarsa zuwa mafi girma a duniya.

Kara karanta wannan

Bayan artabu mai zafi, sojoji sun dakile harin Boko Haram da ISWAP a jihohi 2

A shirin fadada matatar, ya ce za a dauki ma'aikata masu yawa kuma sama da kashi 80 za su kasance 'yan Najeriya.

Dangote ya mika godiya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa yadda ya ke goyon bayan cigaba da tace mai a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng