PDP Ta Yi Wa Sule Lamido Martani Mai Zafi kan Barazanar Kai Ta Kara Kotu
- Rikicin da ke addabar PDP ya dauki sabon salo bayan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi barazanar kai ta kara kotu
- Tsohon gwamnan ya yi barazanar ne bayan ya kasa sayen fom din takarar kujerar shugaban jam'iyyar na kasa
- Sai dai, PDP ta bayyana cewa ba za ta bari wani ko wata kungiya su kawo mata cikas ba a shirin gudanar da babban taron ta da take yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi barazanar maka jam'iyyar PDP mai adawa kara a gaban kotu.
Sule Lamido ya yi barazanar ne bayan ya kasa sayen fom din takarar kujerar shugaban jam'iyyar na kasa.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa jagorancin jam’iyyar PDP ya mayar da martani kan barazanar da Sule Lamido ya yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun da farko Sule Lamido ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar shugaban PDP na kasa.
PDP ta yi wa Sule Lamido martani
PDP ta bayyana cewa ba za ta bari wasu masu neman rigima su kawo tangarda ga shirye-shiryen gudanar da babban taron jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a Ibadan, jihar Oyo, cikin watan Nuwamban 2025.
Mataimakin mai magana da yawun PDP na kasa Ibrahim Abdullahi, ya bayyana cewa jam’iyyar na da niyyar ci gaba da gyara matsalolinta duk da kokarin da wasu ke yi na kawo cikas.
“Mun maida hankali kan abin da zai faru a gaba, kuma ba za mu bari wani ko wata kungiya ta karkatar da hankalinmu daga ci gaba da samun nasara ba."
“A taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da ya gabata, an sanar da ranakun saye da mika fom. Wa’adin mika fom ɗin ya kare ranar 22 ga Oktoba. Duk wanda ya zo bayan wannan lokaci, yana wasan kwaikwayo ne kawai.”
- Ibrahim Abdullahi
Ibrahim Abdullahi ya zargi wasu ‘yan jam’iyya da da kokarin kawo rikici cikin PDP saboda son kansu, inda ya ja hankalin ‘yan jarida da su guji biye musu.
“Shugabannin Arewa sun yanke hukunci. Me ya sa wannan yake da bambanci? Idan (Lamido) yana son zuwa kotu, to ya je."
- Ibrahim Abdullahi

Source: Twitter
Meyasa aka zabi Tanimu Turaki?
Ya bayyana cewa zaɓen Tanimu Turaki a matsayin ɗan takarar maslaha na shugabancin jam’iyya, ya biyo tsarin tarihi da PDP ke bi, inda gwamnoni da manyan jiga-jigan jam’iyya ke yanke hukunci tare.
“A da mutum guda ne ke zabar shugaban jam’iyya. Amma a wannan karon, gwamnoni hudu daga Arewa da wasu fitattun shugabanni sun haɗu suka amince da ɗan takara guda."
"Wadanda suka amfana da wannan tsarin a baya yanzu su ne ke kin amincewa da shi — wannan munafurci ne."
- Ibrahim Abdullahi
Ibrahim Abdullahi ya kara da cewa zuwan Sule Lamido Wadata Plaza maimakon Legacy House, inda ake sayar da fom a hukumance, kokarin kirkirar hayaniya ce kawai don jawo hankalin jama’a.
Turaki ya maida fom din takara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan harkokin na musamman, Kabiru Taninu Turaki, ya mika fom din neman tsayawa takarar shugaban jam'iyyar PDP na kasa.
Kabiru Tanimu Turaki ya wanda ya samu amincewar wasu manyan jiga-jigan PDP, ga mika fom din ne tare da magoya bayansa.
Mika fom din na daga cikin shirye-shiryen da jam'iyyar ke yi don gudanar da babban taron ta a cikin watan Nuwamban 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


