EFCC Ta Bayyana Wasu Yan Kasuwa da Ake Zargi da Daukar Nauyin Ta'addanci a Najeriya
- Shugaban EFCC, Ola Olukoyede ya ce wasu dillalan hakar ma'adanai da duwatsu masu daraja na da hannu a ayyukan ta'addanci a Najeriya
- Olukoyede ya ce ana amfani da wasu yan kasuwa da ke harkar ma'adanai wajen safarar kudin haram da taimakawa 'yan ta'adda
- Ya gargadi yan kasuwa da su guji mu'amala da wadanda suke da shakku a kansu, kuma su rika ba da rahoton don taimakon hukumomi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ibadan, Oyo State – Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta bankado wasu manyan dillalai da take zargin suna da hannu a daukar nauyin ta'addanci a Najeriya.

Kara karanta wannan
Kungiyar Amnesty Int'l ta yi magana da Hisbah ta kama masu shirin 'auren jinsi' a Kano
EFCC ta ce wasu ‘yan kasuwa da masu sana’ar haka da cinikayyar duwatsu da ma’adinai masu daraja na daga cikin wadanda ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci a wasu yankunan kasar nan.

Source: Facebook
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani taron wayar da kai da horaswa na yini guda a Ibadan, cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron dai na shirya shi ne domin horas da masu hakar ma’adinai da ‘yan kasuwar duwatsu masu daraja a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Bugu da kari, bayanai sun nuna cewa an shirya taron ne da hadin gwiwar EFCC da hukumar bayanan kudi ta kasa (NFIU), tare da tallafin hukumar kasar Jamus ta GIZ.
Shugaban EFCC ya fadi masu taimakon yan ta'adda
Olukoyede, ya yi jawabi a taron ta bakin wakilinsa, Toyin Ehindero-Benson, mai kula da sashen yaki da safarar kudi (SCUML) na ofishin EFCC a Ibadan.
Shugaban EFCC ya soki wasu ‘yan kasuwa da ke yin sakaci wajen bin ka’idojin sanin abokan hulɗarsu wajen cinikayyar ma'adanai da duwatsu masu daraja.
Ya ce, rashin bin doka da rashin bayar da rahoton mu’amaloli da ake shakku a kansu na daga cikin dalilan da ke kawo cikas ga yunkurin EFCC na yaki da safarar kudi da daukar nauyin ta’addanci.
EFCC ta gargadi masu harkar ma'adanai
Olukoyede, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya fitar, ya ce:
“Ayyukan wannan masana’anta (ma’adinai) yana da muhimmanci sosai wajen yaki da manyan laifukan kudi.
"Wannan taron ya ba mu damar fadakarwa, musayar dabaru, da karfafa hadin kai tsakanin hukumomi da masu sana’a,” in ji
Ya kuma gargadi masu hakar ma’adinai da ‘yan kasuwar duwatsu masu daraja da su guji bari a yi amfani da su wajen safarar kudaden haram da daukar nauyin ayyukan ta’addanci, kamar yadda PM News ta rahoto.

Source: Facebook
EFCC ta kwato Naira biliyan 500
A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana nasararorin da hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta samu a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Shettima ya ce EFCC ta samu nasarar tara dukiyar da ta kai Naira biliyan 500 cikin shekaru biyu da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi a kan mulki.
Ya ce manufar gwamnatin Tinubu ta rashin tsoma baki a harkokin hukumomin yaki da rashawa ta taimaka wajen karfafa yaki da cin hanci da kuma inganta gaskiya a hukumomin gwamnati.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

