Bola Tinubu Ya Kira Sababbin Hafsoshin Tsaro, Sun Shiga Ganawa a Aso Rock
- Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci taron tsaro na farko bayan sauya manyan hafsoshin tsaron Najeriya
- Rahotanni daga fadar shugaban kasa sun tabbatar da cewa sabbabin hafsoshin tsaron kasar nan sun halarci taron yau Litinin, 27 ga Oktoba, 2025
- Duk da babu wata sanarwa a hukumance da ta bayyana abubuwan da aka tattauna, amma majiyoyi sun ce zaman maida hankali kan tsarin tsaro
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeriya – Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya shiga taron sirri da sababbin hafsoshin rundunonin sojojin Najeriya a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Har kawo yanzu babu wani cikakken bayani kan abubuwan da za a tattauna a wannan taron tsaro, karo na farko bayan Tinubu ya sauya manyan hafsoshin tsaron Najeriya.

Source: Twitter
Bola Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa majiyoyi sun nuna cewa ganawar na da nasaba da ƙoƙarin da ake yi don ƙarfafa tsarin tsaro da inganta aikin rundunonin sojoji a ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan hafasoshin tsaron lasar nan sun halarci wannan taro wanda ke gudana yanzu haka a Aso Rock, yau Litinin, 27 ga watan Agusta, 2025.
Fadar shugaban ƙasa dai ta bayyana cewa nadin sababbin hafsoshin tsaro wani muhimmin mataki ne na inganta tsarin tsaro da ayyukan rundunonin tsaro na Najeriya.
Hafsoshin tsaron da suka halarci taron
Rahotanni sun nuna cewa wadanda suka halarci wannan taron sun haɗa da; Babban Hafsan Tsaro na Kasa, Janar Olufemi Oluyede da Babban Hafsan Rundunar Sojojin Kasa, Manjo Janar Waidi Shaibu.
Haka zalika an ga Babban Hafsan Rundunar Sojojin Sama, Air Vice Marshal Kennedy Aneke Babban Hafsan Rundunar Sojojin Ruwa ta Najeriya, Rear Admiral Idi Abbas sun shiga wannan taro.

Kara karanta wannan
Dalilin Buhari da Tinubu na korar Janar 500 daga rundunar tsaro duk da matsalar ta'addanci
Ana sa ran ganawar za ta mayar da hankali kan tsare-tsaren tsaro, dabarun yaki da ta’addanci da kuma hanyoyin inganta haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan.
Dalilan sauya hafsoshin tsaron Najeriya
Wannan ci gaban ya zo ne ‘yan kwanaki bayan da Shugaba Bola Tinubu ya yi sauye-sauye a manyan hafsoshin sojojin kasar nan, cewar rahoton Channels tv.
A cikin wannan sauyi, Tinubu ya sauke Janar Christopher Musa daga mukaminsa na Babban Hafsan Tsaro, inda ya nada Janar Olufemi Oluyede, wanda a da shi ne Babban Hafsan Sojojin Kasa.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Sunday Dare, ya tabbatar da wannan sauyi, yana mai cewa matakin yana cikin kokarin gwamnatin tarayya na karfafa tsarin tsaron kasa.

Source: Twitter
Babban mai bincike ya yaba wa Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa babban mai bincike a matakin duniya, Oyewole Oginni, ya bayyana cewa sauya manyan hafsoshin tsaro ba abin tada hankali ba ne.
Oginni, babban mai bincike a Cibiyar Nazarin Rikice-rikice ta Duniya da ke Bonn, da ke Jamau ya ce duba da abubuwan da faruwa, Bola Tinubu ya yi abin da ya dace kuma akan lokaci.
Ya bayyana cewa duba da yadda wasu ƙasashen Afirka ke fadawa mulkin soja, da yadda ’yan ta’addan ISWAP ke matsowa Kudu a Najeriya, akwai bukatar sauya tsarin tsaron kasar nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

