Sule Lamido Ya Fuskanci Matsala a Shirin Takarar Shugabancin Jam'iyyar PDP

Sule Lamido Ya Fuskanci Matsala a Shirin Takarar Shugabancin Jam'iyyar PDP

  • Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya nuna takaicinsa kan abin da ya tarar da ya je hedkwatar jam'iyyar PDP
  • Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa an hana shi sayen fom din takarar kujerar shugaban jam'iyyar PDP na kasa
  • Babban 'dan siyasar ya nuna cewa ko kadan hakan bai sace ba kuma ya saba da tsarin dimokuradiyyar jam'iyyar

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya yi barazanar kai karar jam’iyyar PDP a kotu.

Sule Lamido ya yi barazanar ne bayan da aka hana shi samun fom ɗin neman takarar kujerar jam’iyyar PDP na kasa.

Sule Lamido ya yi barazanar kai PDP kara
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido Hoto: Sule Lamido
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce Sule Lamido ya isa hedkwatar jam’iyyar ta kasa da ke Wadata Plaza, Abuja, da safiyar Litinin, 27 ga watan Oktoban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sule Lamido ya ce an hana shi sayen fom

Kara karanta wannan

2027: Sule Lamido zai nemi takarar shugaban jam'iyyar PDP na kasa

Tsohon gwamna ya ce an hana shi siyan fom ɗin, abin da ya bayyana a matsayin ba daidai ba kuma ba tsarin dimokuraɗiyya ba, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da labarin.

Sule Lamido ya bayyana shirinsa na shiga zaben da za a gudanar a babban taron jam’iyyar PDP da za a gudanar a Ibadan, jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga Nuwamban 2025.

Wane mataki zai dauka kan PDP?

Sai dai, ya yi gargadin cewa zai dauki matakin shari’a idan har aka hana shi shiga takara.

“Na zo nan don na sayi fom ɗin kujerar shugabancin jam’iyya, amma an hana ni. Wannan ba ita ce dimokuraɗiyyar da jam’iyyarmu ta tsaya a kanta ba."
“Idan hakan ya ci gaba da faruwa, ba ni da wani zabi face na nemi adalci a kotu.”

- Sule Lamido

Sule Lamido ya bayyana cewa lokacin da ya isa ofishin sakataren tsare-tsare na kasa, inda aka saba sayar da fom, ofishin ya kasance a rufe.

“Na same shi tare da sakataren jam’iyya, Sanata Samuel Anyanwu. Na gaya musu cewa na zo na sayi fom."

Kara karanta wannan

Turaki ya kara fuskantar matsala a shirin zama shugaban PDP na kasa

"Dukkansu suka ce ba su da masaniya a kan inda fom ɗin yake, ko yadda aka buga su, ko kuma yadda ake sayar da su. Hakan ya ba ni mamaki sosai."

- Sule Lamido

Sule Lamido ya yi barazanar maka PDP gaban kotu
Sule Lamido wanda ke neman takarar shugabancin PDP Hoto: Sule Lamido
Source: Facebook

Sule ya koka kan halin da PDP ke ciki

Ya kara da cewa, abin mamaki ne cewa mutumin da ke da alhakin kula da tsarin jam’iyya ma an hana shi shiga ofishinsa, don haka lamarin ya zama abin damuwa.

Sule Lamido ya ce bai ji wata sanarwa ba da ke nuna cewa an canza tsarin sayen fom ɗin, yana mai bayyana batun a matsayin lamarin cikin gida na jam’iyya da bai kamata ya jawo rigima ba.

Ya kuma ce ya je Wadata Plaza bisa ga al’adar jam’iyya, amma tun da lamarin yana hannun kwamitin shirya babban taron wanda Gwamna Ahmadu Fintiri ke jagoranta, to akwai yiwuwar sai ya je Adamawa domin sayan fom ɗin.

Takarar Turaki a PDP ta samu matsala

A wani labarin kuma, jun ji cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Kebbi ta nesanta kanta daga amincewa da Kabiru Tanimu Turaki a matsayin dan takara shugabanta na kasa.

Kara karanta wannan

Wike ya ragargaji gwamnonin PDP, ya fadi illar da za su yi wa jam'iyyar

Ta bayyana cewa ba a tuntube ta ba kafin amincewa da tsohon ministan a matsayin dan takarar shugaban jam'iyyar na kasa.

Hakazalika, ta bukaci kwamitin gudanarwa na kasa na jam'iyyar da ya ba yankin Arewa maso Yamma damar fitar da dan takarar da yake so.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng