Sanata Ned Nwoko Ya Fadi Abubuwa 2 da za Su Dawo da Zaman Lafiya Kudu maso Gabas

Sanata Ned Nwoko Ya Fadi Abubuwa 2 da za Su Dawo da Zaman Lafiya Kudu maso Gabas

  • Sanata Ned Nwoko, wanda ke wakiltar Delta ta Arewa, ya ce zaman lafiya a kudu-maso Gabas ba zai tabbata ba sai gwamnati dauki matakai biyu
  • Sanata Nwoko ya ce sakin shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, da kuma kirkirar jihar Anioma za su taimaka wajen kawo kwanciyar hankali a yankin
  • 'Dan majalisar ya bayyana cewa yankin Kudu maso Gabas na da jihohi biyar ne kawai wanda ke kara tsananta rashin jin dadi wajen kabilar Ibo

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Delta – Sanata Ned Nwoko ya bayyana cewa rashin zaman lafiya da tashin hankali a Kudu maso Gabas ya samo asali ne daga abin da ake ganin rashin adalci daga gwamnatoci.

Ya ce har yanzu akwai damuwa a cikin al’umma saboda yankin na da jihohi biyar ne kawai, wanda hakan ke kara haifar da rashin daidaito da matsalolin siyasa a shiyyar.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ce an yi abin kunya a filin wasan Kebbi da aka gina da kudin FIFA

Ned Nwoko ya ba da shawara kan maganin rikice-rikice
Hoton Sanata Ned Nwoko Hoto: @Prince_NedNwoko
Source: Facebook

A hira da ya yi da Channels TV, Nwoko ya kara da cewa, sakin shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, wanda yake a hannun hukumar DSS tun watan Yuni 2021 zai rage tashin hankali a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata ya shawarci gwamnatin Najeriya

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Sanatan ya bayyana cewa ci gaba da tsare Kanu a hannun gwamnati ba adalci bane kuma ya zama daya daga cikin manyan dalilan tashin hankali a yankin.

Sanata Nwoko, wanda ke jagorantar yakin neman kirkirar jihar Anioma daga jihar Delta, ya ce matakin na samun karbuwa sosai.

Ya bayyana cewa kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da wakilai kan duba tsarin kundin tsarin mulki ya amince da ra’ayin kara jihar daya a Kudu maso Gabas.

Sanata Nwoko ya ce tabbas Tinubu zai amince da samar da jihar Anioma
Sanata Ned Nwoko mai wakiltar Delta ta Arewa Hoto: @Prince
Source: Instagram

Sanatan ya ce a zaman sauraron ra’ayi da aka gudanar a Enugu, an gabatar da hujjojin da suka nuna muhimmancin wannan jihar.

Ya kara da cewa yana da yakinin cewa za a zabi Anioma daga cikin jihohin da ake tantancewa domin kara yawan jihohin Najeriya.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu: Wike ya fadi sharadin zama shaidan shugaban IPOB a kotu

Kiran Sanata Nwoko ga gwamnati

Nwoko ya nuna bayyana cewa yana da yakinin sShugaba Bola Tinubu zai amince da kirkirar jihar idan kwamitin ya bada shawara.

Sanatan ya bayyana cewa kirkirar jihar zai kasance babbar kyauta mafi kyau da shugaban kasa zai iya bayarwa ga al’ummar Igbo.

Nwoko ya ce sakin Kanu da kirkirar jihar Anioma zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya a Kudu maso Gabas, rage rikici, da kuma bude hanyar tattaunawa tsakanin al’umma da gwamnati.

Yadda Sanata ya tausayawa maza

A baya, mun wallafa cewa ]Ned Nwoko ya bayyana cewa yana tausayin maza masu mace ɗaya, yana mai cewa tsarin auren mace ɗaya ba ya samar da kwanciyar hankali ga rayuwar aure.

Sanata Ned Nwoko mai wakiltar Delta ta Arewa ya ce yana alfahari da matansa hudu kuma bai taɓa nadama ba kan yadda ya zaɓi tsarin aurensa na fiye da mace ɗaya ba.

Yana wannan batu ne bayan daya daga cikin matansa, jarumar fina-finan Nollywood, Regina Daniels, ta mallaki sabon gida bayan jita-jitar da ke cewa akwai rashin jituwa da Nwoko.

Kara karanta wannan

John Zuya: 'Yan sanda sun cafke wanda ake zargi da kashe mawakin gargajiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng