NDLEA Ta Gano yadda aka Boye Miyagun Kwayoyi a Robobin Man Shafawa

NDLEA Ta Gano yadda aka Boye Miyagun Kwayoyi a Robobin Man Shafawa

  • Hukumar NDLEA ta gano hodar iblis guda 70 da aka ɓoye a cikin kwalaben man shafawa da ake shirin fitar da su daga Najeriya
  • An kama mutane da dama a Legas, Enugu, Kwara, Taraba, da sauran jihohi yayin da hukumar ke gudanar da samame a faɗin ƙasar
  • Shugaban NDLEA, Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin tare da jan kunne matasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta gano hodar iblis guda 70 mai nauyin kilo 3.6 da aka ɓoye a cikin kwalaben man shafawa.

Hukumar ta ce an gano kayan ne a filin jirgin saman Murtala Muhammed, Ikeja, Lagos, ranar 14 ga Oktoba 2025, yayin duba kaya da ke hanyar zuwa Birtaniya.

Kara karanta wannan

Kungiyar Amnesty Int'l ta yi magana da Hisbah ta kama masu shirin 'auren jinsi' a Kano

Hukumar NDLEA ta kama hodar iblis a Legas
Shugaban NDLEA, Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya da wasu jami'an hukumar Hoto: NDLEA
Source: Facebook

The Guardian ta wallafa cewa Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya ce an kama Lawal Mustapha Olakunle,da aka gani da kayayyakin.

Hukumar NDLEA ta yi babban kame

Vanguard News ta wallafa cewa bincike ya kai ga kama wata jami'ar lafiya, Ogunmuyide Taiwo Deborah da Mutiu Adebayo Adebiyi, shugaban kamfanin tafiye-tafiye “Mutiu Adebiyi & Co.”.

A wani lamari makamancin haka, jami’an NDLEA a filin jirgin sama na Akanu Ibiam, Enugu, sun kama wani ɗan ƙasar Lesotho mai shekaru 35, Lemena Mark.

An kama shi da ƙwayar methamphetamine mai nauyin giram 103.59 da ya ɓoye a cikin shayi mai suna Diabeto’s Herbs yayin da yake ƙoƙarin tafiya zuwa Philippines.

NDLEA ta kama matashi da makami a Zamfara
Hoton Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa mai ritaya Hoto: NDLEA
Source: Twitter

A Legas, jami’an NDLEA sun kai samame a Proxy Nightclub, Victoria Island, inda suka kama sama da mutum 100, ciki har da mai gidan, shahararren dan Lagos, Pretty Mike.

An kwace kwalayen wani irin tabar wiwi bayan samun bayanan sirri cewa kulob ɗin na shirya bukukuwa masu alaƙa da miyagun ƙwayoyi.

Kara karanta wannan

An dawo da 'yan Najeriya 150 da suka makale a kasar Nijar

A Kwara, an kama Umar Abubakar da ƙwayoyi 21,950 na tramadol, yayin da a Taraba, an cafke Auwal Musa da Salihu Bala da kwayoyi 450,000 na tramadol da Exol-5.

NDLEA ta kama kwayoyi da dama

Haka kuma, jami’an NDLEA sun gano kilo162 na skunk a hanyar Okene–Lokoja, yayin da aka kama wasu kilo 128 a Keffi, Nasarawa.

A Lekki, an kama Oyonumoh Glory Effiong da giram 500 na wiwi sannan a Ikorodu, jami’an sun gano lita 275 na wasu nauyin kwayoyi hade da wiwi.

A Abia, wani tsoho mai shekaru 75, Echendu Onuoka, da wata mata mai shekaru 60, Aukana John, sun shiga hannu da wiwi mai nauyin kilo 4.7.

A Zamfara, jami’an sun kama Abubakar Ibrahim mai shekaru 30 da bindigar AK-47 da harsasai 1,746.

Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa (rtd.), ya yaba wa jami’an da suka gudanar da wadannan ayyuka, yana mai cewa hukumar za ta ci gaba da yaƙar fataucin miyagun ƙwayoyi.

Jami'an NDLEA sun kama wiwi a Kano

A baya, kun ji cewa jami’an NDLEA sun gano wani mota mai ɗauke da tabar wiwi kilo 112, bayan motar Volkswagen bayan da aka yi rashin sa'a motar ta yi hatsari a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Injiniyoyi sun ga kokarin Gwamna Abba, sun ba shi lambar girmamawa

Jami’an hukumar sun bayyana cewa sun garzaya wurin haɗarin da yamma domin ceto rayuka da bayan sun ji alamun cewa an samu hadarin mota, sai suka kama kwayoyi.

Direban ya bayyana cewa yana wakilin mai na kaya ne, kuma ya bi hanyar ta hannu daya don kaucewa shingen duba kayan NDLEA, wanda haka ne kuma ya jawo hadarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng