Sarki Sanusi II Zai Jagoranci Taron Duniya a gaban Gwamnoni da Ministoci
- Sarki Muhammadu Sanusi II da Atedo Peterside za su jagoranci babban taron shugabanci na Oxford Global Think Tank
- Taron zai gudana ne a ranar Talata, 28, Oktoba, 2025 a dakin taron Congress Hall na otel din Transcorp a birnin Abuja
- Rahoto ya ce za a tattauna kan shugabanci nagari da yadda za a iya sauya tsarin jagoranci domin ciyar da Najeriya gaba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – An shirya wani babban taron shugabanci da Oxford Global Think Tank ke daukar nauyi, wanda Sarki Muhammadu Sanusi II da Atedo Peterside za su jagoranta.
Taron da za a yi a ranar Talata, 28, Oktoba, 2025, na da nufin kara habaka tattaunawa tsakanin bangarorin gwamnati, masu zaman kansu da kungiyoyin farar hula.

Source: Twitter
The Cable ta wallafa cewa shugaban shirye-shiryen taron, Williams Eze ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Williams Eze ya bayyana cewa taron zai mayar da hankali ne kan shugabanci nagari, gaskiya da hadin kai wajen gina makomar Najeriya.
Alakar taron da shugabanci a Najeriya
A cewar Eze, taron zai hada manyan masana da shugabanni daga sassa daban-daban domin nazarin tafiyar shugabanci a Najeriya bayan shekaru 65 da samun ’yancin kai.
Ya ce za a kuma duba matsalolin da suka fi dabaibaye tsarin mulki da shugabanci a kasar tare da fitar da sababbin dabaru don tabbatar da daidaito da sauyi mai amfani ga kasa.
Daily Trust ta wallafa cewa taron zai zama wata kafa ta tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki domin samar da hanyoyin jagoranci masu inganci da dorewa.
Manyan baki da za su halarci taron
Ana sa ran tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo; tsofaffin Shugabannin Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da Anyim Pius Anyim za su halarta.
Haka zalika ana sa ran mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu; da gwamnan jihar Abia, Alex Otti, za su kasance baki na musamman.

Source: Twitter
Haka kuma, ministoci da shugabannin manyan cibiyoyin kudi, karamar ministar kudi, Doris Uzoka-Anite, shugabar bankin Fidelity Nneka Onyeali-Ikpe za su hallara.
Taron zai hada shugaban bankin Sterling, Abubakar Suleiman, da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, kuma za su gabatar da jawabi.
Masu shirya taron sun ce mahalarta za su yi nazari kan batutuwan da suka shafi shugabanci, tattalin arziki da fasaha.
Za a kaddamar da littafi a taron
A yayin taron, Oxford Global Think Tank za ta kaddamar da rahotonta na farko kan ma’adanan Afirka.
Haka kuma, wacce ta kafa cibiyar Arunma Oteh, za ta gabatar da littafinta mai taken “All Hands on Deck: Unleash Prosperity through World-Class Capital Markets.”
Ta wallafa littafin ne domin karfafa tunani kan yadda Afirka za ta bunkasa ta hanyar ingantacciyar kasuwar hada-hadar kudi.
Sarki Sanusi II ya gana da kamfanonin China
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya ziyarci kasar China kuma ya tattauna da wasu kamfanoni.
Mai martaban ya ce sun tattauna da kamfanonin ne domin duba yiwuwar shiga wasu lamura na Kano a shirin kawo cigaba jihar.
Sarki Sanusi II ya bayyana cewa Kano na shirin hadaka da kamfanonin wajen inganta lantarki da tsaro a jihar domin kawo cigaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


