Hawan Dawaki: Gwamna Abba Kabir Ya ba Sarakunan Kano Umarni, Sanusi II Ya Yi Godiya
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya farantawa sarakunan gargajiya a Kano rai bayan umarnin da ya ba su domin habaka al'adu da ci gaban al'umma
- Abba Kabir Yusuf ya umarci dukkan sarakunan Kano da su ci gaba da gudanar da bikin hawan dawaki domin kare al’adun gargajiya
- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yaba da kokarin gwamnatin jihar wajen farfado da al’adun Kano tare da karfafa dangantaka da al’umma
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya ba da umarni ga sarakunan gargajiya a jihar kan hawan dawaki duk shekara domin inganta al'adunta.
Abba Kabir Yusuf ya umarci sarakunan jihar da su ci gaba da gudanar da bikin hawan don kare al’ada da kuma inganta su.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a shafin Facebook a yammacin yau Asabar 25 ga watan Oktobar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkawarin da Abba Kabir ya yi ga masarautu
Abba ya ce gwamnati za ta tallafa wa masarautu wajen tabbatar da wannan tsohon al’ada ta hawan dawaki domin duniya ta san darajar Kano.
Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce Abba Yusuf ya bayar da wannan umarni a wajen bude taron Kanfest (Kalankuwa) na shekarar 2025 da muke ciki a Kano.
An shirya taron KANFEST domin murnar bambancin al’adu, karfafa matasa da mata, da kuma hadin gwiwar duniya wajen tallata al’adun Kano.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari wajen raya fasaha, al’adu da yawon bude ido domin hadin kai da ci gaban tattalin arziki.
A cewarsa, inganta al’adu zai taimaka wajen samar da cigaba da kuma karfafa sha’awar matasa da masu fasaha su taka rawarsu.
Wannan umarni na gwamnan ya farantawa sarakuna rai duba da muhimmancin al'adu da kuma tasirin da suke da shi a kan ci gaban kasa.

Source: Facebook
Sakon godiya daga Sanusi II ga Abba Kabir
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yaba da hangen nesa na gwamnatin jihar wajen dawo da tsofaffin al’adun Kano masu daraja.
An gudanar da bikin na tsawon kwanaki uku inda aka nuna kayan gargajiya, abinci na gida, wasanni, wasan kwaikwayo da nunin kayan fasaha.
Taron ya jawo hankalin masu sarauta, jakadu, matasa, masu fasaha, kungiyoyin gargajiya da masu zuba jari daga cikin gida da kasashen waje wanda ake ganin zai ba da damar sake bunkasa tattalin arzikin Kano.
'Yan sanda sun hana hawan sallah a Kano
A baya, mun ba ku labarin cewa rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta sanar da haramta duk wani hawan Sallah a bukukuwan sallah karama, domin tabbatar da doka da oda.
Kwamishinan 'yan sanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne saboda karuwar rashin jituwa a jihar.
Bakori ya gargadi Musulmi da su bi dokokin tsaro, ciki har da guje wa tukin ganganci da hawan doki, tare da kiyaye dokar da aka gindaya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


