Kwararren Mai Bincike Ya Gano Dalilan Korar Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya
- Tun bayan matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauka na sauya manyan hafsoshin tsaro aka fara ce-ce-ku-ce kan dalilan hakan
- Wasu na ganin hakan na da alaka da jita-jitar da aka yada kwanakin baya cewa an kama wasu sojoji na yunkurin juyin mulki
- Sai dai wani babban mai bincike, Oyewole Oginni, ya musanta jita-jitar da mutane ke yadawa, ya ce Tinubu ya yi abin da ya dace a kan lokaci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria – Babban mai bincike a Cibiyar Nazarin Rikice-rikice ta Duniya da ke Bonn, Oyewole Oginni, ya bayyana cewa sauya manyan hafsoshin tsaro ba abin tada hankali ba ne.

Kara karanta wannan
Tsohon janar ya fadi abin da zai faru a gidan soja bayan Tinubu ya yi sauye sauye
Kwararren mai binciken ya danganta matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kora da nada sababbin hafsoshin tsaro da batun kimanta aiki, wanda a cewarsa abu ne na al’ada a tsarin mulki.

Source: Facebook
Oginni ya yi wannan furucin ne a wata hira da aka yi da shi a cikin shirin Mornin Show na tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya yi sauye-sauye a rundunonin sojojin Najeriya a ranar Juma’a, abin da wasu ke ganin yana da nasaba da rahotannin jita-jitar yiwuwar juyin mulki.
Abin da babban mai binciken ya hango
Sai dai a hirar da aka yi da shi ranar Asabar, Oginni ya karyata wannan zato, yana cewa sauye-sauyen sun dace da yanayin tsaro a yankin Sahel, inda yake ganin ya zama dole gwamnati ta dauki mataki.
“A gani na, babu wani sabon abu ko wani boyayyen dalili a cikin wannan. Ba abin firgici ba ne, kuma abu ne da ya kamata ya faru.
"Sauya hafsoshin taaro yana da alaƙa da kimanta aiki da sauyin dabaru bisa yanayin da ake ciki. Dole ne a sabunta tsarin tsaro lokaci zuwa lokaci domin fuskantar kalubalen da ke tasowa.”
- Oyewole Oginni.
Oginni ya tabo batun juyin mulki
Oginni ya bayyana cewa duba da yadda wasu ƙasashen Afirka ke fadawa mulkin soja, da yadda ’yan ta’addan ISWAP ke matsowa Kudu a Najeriya, Shugaba Tinubu ya yi abin da ya dace.
A cewarsa:
“Dole ne shugaba mai hangen nesa ya kalli abin da ke faruwa a ƙasashen makwabta, kuma ya dauki mataki kafin abubuwa su kai bango.
"Ko da akwai jita-jitar juyin mulki ko babu, wajibi ne gwamnati ta lura da yanayin da ke kewaye da ita.”

Source: Twitter
Ya kawo misalin abin da ya faru a Madagascar, inda zanga-zanga ta rikide zuwa juyin mulki, yana cewa, “Wannan na nuna yadda abubuwa ke iya sauyawa cikin lokaci."
Dalilan Tinubu na korar hafsoshin tsaro
Kuna da labarin, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa sauya hafsoshin tsaro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi, ba shi da alaka da jita-jitar yunkurin juyin mulki.
Ta ce korar da aka yi wa tsofaffin hafsoshin tsaro da nada sababbi, wani mataki ne da aka dauka domin kawo sabon shugabanci da kuzari ga hukumomin soji.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: Fadar shugaban kasa ta fadi dalilin Tinubu na korar hafsoshin tsaro
Fadar ta ce Shugaba Tinubu ya yi amfani da ikon da doka ta ba shi a matsayin kwamandan asakarawan Najeriya wajen sauya shugabannin sojoji.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
