Gwamnan Kogi Ya Yabi Hangen Nesan Tinubu da Ya Nada 'Dan Jiharsa Hafsan Sojan Kasa
- Gwamna Kogi, Usman Ododo ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa canjin da ya yi a shugabancin rundunar sojan Najeriya
- Gwamna Ododo ya kuma bayyana jin dadin nadin ɗan asalin jiharsa, Manjo Janar Waidi Shaibu, a matsayin Babban Hafsan Sojan Ƙasa
- Ododo ya bayyana cewa wannan nadi ya nuna tsantsar adalci da girmama cancanta wajen hidimar ƙasa da Tinubu ya ke da shi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kogi – Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Usman Ododo, ya jinjinawa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa sababbin nade-naden da ya yi a rundunar sojan Najeriya.
Gwamnan ya ji dadin yadda Tinubu ya nada Manjo Janar Waidi Shaibu, ɗan asalin jihar Kogi, a matsayin sabon Babban Hafsan Sojan Ƙasa, COAS.

Kara karanta wannan
Tsohon janar ya fadi abin da zai faru a gidan soja bayan Tinubu ya yi sauye sauye

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Shugaba Tinubu ya amince da manyan sauye-sauye a shugabancin rundunonin tsaron ƙasar a ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya ni sababbin nade-nade
Daily Post ta wallafa cewa sabon hafsan soja, Manjo Janar Shaibu, ya maye gurbin Laftanar Janar Olufemi Oluyede, wanda aka ɗaga zuwa mukamin Babban Hafsan Tsaron Ƙasa (CDS).
Haka kuma, Air Vice Marshal Sunday Kelvin Aneke ya zama sabon Hafsan Sojan Sama, yayin da aka nada Rear Admiral Idi Abbas a matsayin sabon Hafsan Rundunar Ruwa.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan bayanai da sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya fitar a ranar Juma’a, Gwamna Ododo ya bayyana nadin da Tinubu ya yi.

Source: Twitter
Ya ce nadin Manjo Janar Shaibu a matsayin tabbacin jajircewar Shugaba Tinubu wajen tabbatar da adalci da karrama cancanta a ayyukan ƙasa.
Ododo ya ce samun ɗan asalin Kogi a irin wannan matsayi babban abin alfahari ne ga mutanen jihar, inda ya jaddada cewa kwalliya za ta biya kudin sabula.

Kara karanta wannan
Janar Undiandeye: Sojan da ya tsira da kujerarsa da Tinubu ya kori hafsoshin tsaro
Gwamna ya yabi sabon Hafsun tsaro
Gwamnan ya nanata cewa kwarewa, ladabi, da jajircewar Manjo Janar Shaibu wajen aikinsa ne suka bambanta shi da sauran jami'ai.
A kalamansa:
“Manjo Janar Shaibu jajirtacce ne mai ƙwarewa wanda tarihin aikinsa ya tabbatar mana cewa zai ci gaba da yin aiki tukuru wajen inganta tsaron ƙasa."
Gwamnan ya kuma bayyana tabbacin cewa sabon Babban Hafsan Sojan Ƙasa zai ƙara ƙarfafa rundunar sojan ƙasa tare da inganta tsaron baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa:
“Muna da cikakken tabbaci cewa Manjo Janar Shaibu zai mutunta amincewar da aka yi masa ta hanyar aiwatar da aikinsa cikin gaskiya da nasara.”
Ododo ya taya sabon hafsan soja murna tare da tabbatar wa da gwamnatin Tinubu cewa mutanen Kogi za su ci gaba da ba ta cikakken goyon baya da biyayya.
ADC ta nemi bayani kan canja hafsoshin tsaro
A baya, kun ji cewa a jam'iyyar ADC ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya bayyana wa ’yan Najeriya ainihin dalilan da suka sa ya sauya hafsoshin tsaro cikin gaggawa.
A ranar Jumma’a, 24 ga watan Oktoba, 2025, Shugaban kasa, Bola Tinubu ya kori tsofaffin hafsoshin tsaro tare da nada sababbi domin jagorantar rundunonin tsaron kasar.
Mallam Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa jam’iyyar na ganin sauyin ya zo ne a wani lokaci mai cike da rudani, musamman bayan jita-jitar da ke yawo game da yunkurin juyin mulki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
