Ranar Haihuwa: Kwankwaso Ya Ji Dadin Abin da Tinubu, IBB, Atiku Suka Masa
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna godiya ga shugabanni da dama da suka taya shi murnar cika shekara 69
- Ya bayyana farin cikinsa bisa irin sakonnin fatan alheri daga shugabanni, abokai da magoya baya a fadin kasa
- Tsohon gwamnan Kano ya mika godiya ta musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu da mai girma Atiku Abubakar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna matukar farin ciki da godiya ga Allah bisa damar da ya ba shi ya ga cika shekara 69 cikin koshin lafiya.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake nuna godiya ga shugabanni, abokai, ‘yan siyasa da magoya bayansa da suka taya shi murnar rana mai muhimmanci a rayuwarsa.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, Kwankwaso ya ce yanzu lokaci ne na godiya, musamman bisa irin goyon baya da sakonnin fatan alheri da ya samu daga manyan mutane a Najeriya da wajen ta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwankwaso ya godewa Tinubu, Atiku
A cikin sakonsa, Kwankwaso ya fara da godiya ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa kalaman fatan alheri da ya aiko masa.
Haka zalika ya yi godiya ga tsofaffin shugabannin kasa; Janar Olusegun Obasanjo, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, Janar Abdulsalami Abubakar da Goodluck Jonathan.
Haka kuma ya bayyana godiya ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, da Janar T.Y. Danjuma saboda irin kulawa da goyon bayansu.

Source: Twitter
Ya kara jinjinawa ‘yan siyasa da dama ciki har da Sanata Bukola Saraki, tsohon gwamnan Anambra Peter Obi, da wasu tsofaffin gwamnoni da ministoci da suka nuna zumunci da taya murna.
Godiya ga gwamnatin Kano da NNPP
Kwankwaso ya nuna godiya ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa irin goyon baya da ya nuna masa a cikin kwanakin da suka gabata.
Ya kuma yaba da gudunmuwar mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, shugaban majalisar dokokin Kano, Rt. Hon. Jibrin Falgore,

Kara karanta wannan
Shehu Sani ya hango matsalar da za a fuskanta idan Tinubu ya gaza a mulkin Najeriya
Rabiu Musa Kwankwaso ya yi godiya ga Sanata Rufai Sani Hanga mai wakiltar Kano ta tsakiya, da sauran mambobin Majalisar zartarwa ta jihar Kano.
Bugu da kari, ya nuna jin dadinsa ga shugabannin jam’iyyar NNPP a matakin kasa da jiha, ciki har da tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Isaac Idahosa.
Kwankwaso ya mika godiya ga tsohon shugaban jam’iyyar, Dr. Boniface Aniebonam, da shugaba mai-ci, Hon. Ajuji Ahmed.
Godiya ga shugabanni, ‘yan kasuwa a Kano
Kwankwaso ya yi godiya ta musamman ga shugabannin kananan hukumomi da kungiyar ALGON a karkashin jagorancin Hajiya Sa’adatu Yushau Soja.
Kamar yadda aka sani Hajiya Sa’adatu Yushau Soja ce shugabar karamar hukumar Tudun Wada a Kano.
Tsohon 'dan takarar shugaban kasar ya kuma gode wa masu ba da shawara, daraktoci, da shugabannin hukumomi a jihar, da kuma ‘yan kasuwa, musamman Alhaji Nasiru Danfaranshi.
An yi wa Seyi Tinubu addu'o'i a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiya a jihar Kano ta shirya taron addu'a ga dan shugaban kasa Seyi Tinubu bayan cika shekara 40.
Malamai da jama'a sun gudanar da addu'o'i bayan sallar Juma'a a unguwar Sabon Gari da ke jihar Kano.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun ce suna godiya ga dan shugaban kasar bisa kokarin da ya yi wajen samawa matasa ayyuka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

