Magana Ta Fito: Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Dalilin Tinubu na Korar Hafsoshin Tsaro
- Ana ci gaba da tsokaci kan matakin da Shugaba Bola Tinubu ya dauka na sauya kusan dukkanin hafsoshin tsaron Najeriya
- Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa korar da Shugaba Tinubu ya yi musu, ba ta da alaka da jita-jitar yunkurin juyin mulki
- Ta bayyana cewa Mai girma Bola Tinubu yana da ikon nadawa tare da korar duk wanda ya ga dama idan ya bukaci yin hakan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa sauya hafsoshin tsaro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi, ba ya da alaka da jita-jitar yunkurin juyin mulki.
Fadar shugaban kasa ta ce korar da aka yi musu, wani mataki ne da aka dauka domin kawo sabon shugabanci da kuzari ga rundunonin tsaro.

Source: Twitter
An kare Tinubu kan korar hafsoshin tsaro
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan ga jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayo Onanuga ya ce Shugaba Tinubu ya yi amfani da ikon da doka ta ba shi a matsayin kwamandan rundunonin sojoji wajen sauya shugabannin domin inganta aikin tsaro.
“Shugaban kasa yana da cikakken iko na nada ko cire hafsoshin tsaro. Shi ne kwamandan rundunar sojoji. Yana da ikon nadawa da kora."
- Bayo Onanuga
Meyasa Tinubu ya kori hafsoshin tsaro?
A nasa bangaren, babban mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Tope Ajayi, ya bayyana cewa sauyin ya biyo bayan shekaru biyu na aiki a karkashin tsofaffin hafsoshin tsaro.
Ya ce manufar Tinubu kan korar, ita ce kawo sabon salo, hangen nesa da kuzari cikin tsarin tsaro.
“Wannan ba martani ba ne ga jita-jitar juyin mulki. Shugaban kasa yana yin aikinsa bisa doka. Shugabannin sun shafe shekaru biyu a kan mukaman"
- Tope Ajayi
Ya kara da cewa gwamnati na fuskantar matsalolin tsaro a yankuna daban-daban, Boko Haram a Arewa maso Gabas da kuma ’yan bindiga a Arewa maso Yamma.
Har ila yau ya ce akwai 'yan IPOB da ESN a Kudu maso Gabas, garkuwa da mutane a Kudu maso Yamma, da kuma rikice-rikice a Arewa ta Tsakiya.
Gwamnati na kashe kudi kan tsaro
Ajayi ya bayyana cewa yawan kudin da ake kashewa kan harkokin tsaro ya yi yawa a cikin shekaru 15 da suka wuce, abin da ya rage kudin da ake iya amfani da su wajen inganta sauran sassa na tattalin arziki.
“A cikin shekaru 15 da suka wuce, ku duba kasafin kudin kasa, tsaro ne ke daukar kaso mafi tsoka."
"Shugaban kasa yana son magance wannan matsala gaba daya, domin kudin da ake kashewa a harkar tsaro ya koma kan manyan ayyuka kamar wutar lantarki, hanyoyi, ilimi da kiwon lafiya."
- Tope Ajayi

Source: Twitter
Ajayi ya kara da cewa duk wanda shugaban kasa ya nada, ko minista ne, ko shugaban hukuma, ko hafsan tsaro, yana aiki ne bisa amincewar shugaban kasa, ba tare da tabbacin wa’adin aiki ba.
“Kowane jami’in gwamnati yana aiki ne a karkashin amincewar shugaban kasa. Ba wanda ke da tabbacin wa’adin aiki sai shugaban kasa da mataimakinsa kawai."

Kara karanta wannan
Magana ta kare: Kotun Koli ta shirya raba gardama kan dokar ta bacin da Tinubu ya sa a Rivers
- Tope Ajayi
ADC ta magantu kan sauya hafsoshin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa ta yi tsokaci kan sauya hafsoshin tsaro da Shugaba Bola Tinubu ya yi.
ADC ta bukaci shugaban kasa da ya fito ya gayawa 'yan Najeriya gaskiyar dalilin da ya sa ya sauya hafsoshin tsaron.
Jam'iyyar ta nuna shakku kan cewa sauyin na zuwa ne bayan an yada batun jita-jitar yunkurin yin juyin mulki a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

