Fadar Shugaban Kasa Ta Fitar da Sabon Farashin Kayan Abinci a Najeriya

Fadar Shugaban Kasa Ta Fitar da Sabon Farashin Kayan Abinci a Najeriya

  • Fadar shugaban kasa ta ce an samu ragin farashin kayan abinci da ya kai tsakanin kashi 45 zuwa 52 cikin 100 a faɗin ƙasar nan
  • Ta ce manufofin tattalin arzikin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne suka taimaka wajen inganta samar da abinci da rage farashi
  • Gwamnati na ganin saukar farashin a matsayin tabbaci na cigaban tattalin arziki da dorewar wadata ga ‘yan ƙasa baki daya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Fadar shugaban kasa ta ce an samu gagarumin sauƙi a farashin kayan abinci a faɗin Najeriya.

Ta bayyana cewa lamarin na da alaka da cigaban manufofin tattalin arzikin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Kayan abinci a Najeriya
Wajen da ake sayar da kayan abinci a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hadimin Tinubu, Sunday Dare ya wallafa a X cewa raguwar farashin ta shafi muhimman kayan masarufi irin su masara, shinkafa, wake, albasa, tumatur, da manja.

Kara karanta wannan

ADC ta aika sako mai zafi ga Tinubu kan sauya hafsoshin tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa lamarin ya nuna yadda manufofin gwamnati ke haifar da sauƙi ga rayuwar talakawa da kuma inganta samar da abinci a ƙasar.

Yadda farashin kayan masarufi ya ragu

Rahotanni daga ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai sun ce farashin buhun masara ya sauka daga N90,000 zuwa N30,000.

Sunday Dare ya kara da cewa farashin shinkafa 'yar gida ya sauka daga N95,000 zuwa N40,000 a kasuwanni.

Ya ce wake ya sauka daga N150,000 zuwa N85,000, albasa daga N202,500 zuwa N84,000, tumatur daga N155,000 zuwa N65,000, da kuma manja daga N35,000 zuwa N28,000.

Rahoton ya ce buhun dankalin turawa ya sauka daga N140,000 zuwa N30,000, yayin da borkono ya sauka daga N45,000 zuwa N37,000.

Dare ya bayyana hakan a matsayin nasarar da ke nuna yadda tattalin arzikin ƙasa ke murmurewa daga matsin lambar hauhawar farashi.

Tasirin saukar farashi ga 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

Zaben 2027: ICAN ta yi hangen nesa, ta gano babbar barazana ga darajar Naira

Fadar shugaban kasa ta ce raguwar farashin ya bai wa miliyoyin ‘yan Najeriya damar samun abinci cikin sauƙi, wanda hakan ke rage yunwa da inganta gina jiki.

Haka kuma, ya danganta saukar farashin da karuwar amfanin gona, ingantattun hanyoyin sufuri da tallafin da gwamnati ke bai wa manoma a fannoni daban-daban.

Dare ya ce tattalin arziki ya cigaba

Fadar shugaban kasa ta ce raguwar farashin kayan abinci ya kara ƙarfafa kasuwanci, ya farfaɗo da ƙwarin gwiwar ‘yan kasuwa da kuma rage matsn tattalin arziƙi.

Bola Tinubu, Sunday Dare
Tinubu da hadiminsa da ya fitar da bayanai kan farashin abinci. Hoto: Sunday Dare
Source: Twitter

Sunday Dare, ya ce:

“Saukar farashin kayan abinci hujja ce ta cewa jagorancin tattalin arzikin Bola Ahmed Tinubu yana haifar da sakamako mai gamsarwa.”

Dare ya ƙara bayyana cewa cigaban ya nuna yadda gwamnati ke tabbatar da dorewar samar da abinci, tallafa wa manoma, da ƙarfafa masana’antu masu sarrafa kayan gona.

Farashin abinci ya sauka a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa bincike ya nuna cewa farashin kayan abinci ya yi kasa warwas a kasuwannin birnin Abuja da kewaye.

A kasuwar Gwagwalada, Abaji, Kwali da sauransu farashin masara, shinkafa, wake da sauran kayan abinci sun yi kasa sosai.

Kara karanta wannan

Ghana: Matar tsohon shugaban kasa ta riga mu gidan gaskiya tana da shekaru 79

Wasu dillalai da 'yan kasuwa sun bayyana cewa samun amfanin gona mai yawa da kuma karancin kudi na cikin dalilan saukar farashin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng