Janar Musa Ya Bar Hafsun Tsaro ba Tare da Cika Alkawarin Cafko Bello Turji ba

Janar Musa Ya Bar Hafsun Tsaro ba Tare da Cika Alkawarin Cafko Bello Turji ba

  • Shugaba Bola Tinubu ya sallami hafsoshin tsaron Najeriya, ciki har da hafsun tsaron kasa, Janar Christopher Musa
  • Janar Musa ya bar hafsun tsaro ba tare da cika alkawarin da ya dauka na kama rikakken dan bindiga, Bello Turji ba
  • Dama can, Janar Musa ya ce rashin hadin kai da samun bayanan sirri daga al’umma sun taka rawa wajen hana kama Turji

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsige shugabannin rundunonin tsaro na kasa a wani yunkuri na ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya.

Wannan sauyi, ya sa an fara tunawa da alkawarin da tsohon Hafsan Tsaron Kasa (CDS), Janar Christopher Musa, ya dauka a baya (wanda bai cika ba), na kama Bello Turji.

Janar Christopher Musa ya gaza cika alkawarin kamo Bello Turji har Tinubu ya sallame shi daga aiki
Hoton Bello Turji da Janar Christopher Musa. Hoto; @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Janar Musa da alkawarin kama Turji

A ranar Talata, 10 ga watan Satumba, 2024, jaridar Vanguard ta rahoto Janar Musa ya bayyana wa manema labarai cewa:

Kara karanta wannan

Sauya manyan sojoji zai iya jawo sama da Janar 60 su yi murabus a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Babu makawa za mu kama Bello Turji. Ina ba ku tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za mu kamo shi.”

Tsohon hafsan tsaron ya kara da cewa:

"Game da batun Turji, kamar yadda na fada, shi wani bugagge ne da ke ganin yana da karfin iko yanzu, amma ina tabbatar maku, karshensa ya kusa.
"Za mu kama shi nan ba da jimawa ba, za mu kawo karshen wannan ta'addancin da yake yi, na ba ku wannan tabbaci."

Sai dai watanni bayan wannan furuci, har Turji yanzu yana nan yana cin karensa babu babbaka, tare da ci gaba da kai hare-hare a yankunan Arewa maso Yamma.

Yadda Bello Turji ke kai hare-hare a Arewa

Bello Turji, wanda aka dade ana nema ruwa a jallo, ya zama daya daga cikin fitattun jagororin ’yan ta’adda da ke da alaka da manyan kungiyoyin ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da sababbin hafsoshin tsaron Najeriya a Aso Rock

Rahotanni sun nuna cewa Turji na da sansanoni da dama a cikin dajin Kagara da yankin Shinkafi, inda ake zargin yana gudanar da haramtattun ayyuka da suka hada da satar shanu, garkuwa da mutane, da kuma karbar haraji daga kauyuka.

Janar Musa ya fadi matsalar al’umma

A lokacin da yake jagorantar rundunonin tsaro, Janar Musa ya yi bayanin cewa daya daga cikin manyan matsalolin da ke hana nasara a yaki da ’yan ta’adda shi ne rashin goyon baya daga al’umma.

“Muna fama da matsalar masu ba ’yan ta’adda bayanan sirri. Su ne ke nuna musu lokacin da dakarunmu ke motsi. Wannan shi ne abin da ke janyo mana cikas."

- Janar Christopher Musa.

Ya kara da cewa, yakin da ake yi da ’yan ta’adda ba tare da makami ba, yana da matukar wahala saboda ’yan ta’adda suna rayuwa ne cikin al’umma, kuma sojoji ba su san su a ido ba.

“Idan ba mu samu cikakken goyon bayan jama’a ba, za mu ci gaba da yin yakin ne a makance, domin suna rayuwa a cikin jama'a ne."

- Janar Christopher Musa.

Tinubu ya sallami hafsoshin tsaro

A ranar Juma'a ne fadar shugaban kasa ta sanar da cewa Shugaba Tinubu ya kori shugabannin tsaro, ciki har da Janar Musa.

Kara karanta wannan

"Ba zan boye komai ba," Wike ya fadi abin da zai fadawa Jonathan kan batun takara a 2027

Sanarwar ta zo ne bayan wata jita-jita da ta karade kasar, cewa wasu jami'an sojoji sun shirya kifar da gwamnatin Tinubu, kuma har ma an kama wasu daga ciki, zargin da hedikwatar tsaro ta karyata.

Mun ruwaito cewa, Shugaba Tinubu ya ce:

"Ina godiya ga Janar Christopher Musa da tsofaffin shugabannin tsaro saboda sadaukarwarsu. Ina kira ga sababbin hafsoshi su nuna ƙwarewa, aiki tukuru da kuma haɗin kai tsakaninsu.”

Sababbin hafsoshin tsaro za su kakkabe Turji?

Yanzu da Tinubu ya nada sababbin hafsoshin tsaro, tambayar da ke gaban al’umma ita ce: Shin sababbin hafsoshin za su iya kawo karshen Turji da sauran jagororin ’yan ta’adda?

Wani rahoto na Research Gate ya nuna cewa dole gwamnati ta duba tattalin arziki, rashin aikin yi da matsalolin zamantakewa a matsayin tushen ta’addanci.

“Matsalar tsaro a yau a batu ake na makami. Batu ne tattalin arziki da matsalar abinci.
“‘yunwa da talauci sun tashi daga iya matsaloli na yau da kullum na al’umma sun zama barazana tsaron Najeriya.”

- Janar Christopher Musa.

"Shawara ga sababbin hafsun tsaro" - Nura

Wani matashi daga Katsina, Nura Haruna Maikarfe, ya bayyana damuwa game da yadda matsalar tsaro ta gagara zuwa karshe a Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Sunayen sababbin hafsoshin tsaro da Tinubu ya nada bayan korar su Janar Musa

Nura ya ce sauya hafsoshin tsaro zai iya zama wata babbar hanya ta kawo sauyi a tsarin tsaron kasar, musamman ganin cewa "kwararru ne aka nada a kan mukaman."

"Shi sabon hafsan sojin kasa yana da kwarewa sosai, saboda irin namijin kokarin da ya yi a yaki da 'yan ta'adda a Arewa maso Gabas ya sa nake da yakinin cewa zai iya kawo karshe ire-irensu Bello Turji a cikin kankanin lokaci.
"Shi da ma yaki sai da jagora, kuma an shaida cewa sabon hafsan sojan ya na da kwarewar jagorancin dakaru zuwa fagen daga, don haka zai iya kashe Turji cikin karamin lokaci."

- Nura Haruna.

Matashin ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da dukkanin kayayyakin tsaro da sojoji ke bukata sannan a inganta walwalar jami'an don kara masu hazakar aiki.

Janar Oluyede ya maye gurbin Janar Musa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, a ranar Juma'a, 24 ga watan Oktoba, 2025, Shugaba Bola Tinubu ya kori hafsoshin tsaron Najeriya tare da nada sababbi.

Daga cikin hafsoshin tsaron da aka sallama, akwai Janar Christopher Musa, wanda yake rike da mukamin babban hafsan tsaro na kasa (CDS).

Kara karanta wannan

Fasahar AI za ta kawo matsala a ayyukan mutane? Sheikh Isa Pantami ya yi bayani

Sababbin hafsoshin tsaron da Tinubu ya nada sun hada da Janar Olufemi Oluyede, wanda ya maye gurbin Janar Christopher Musa a matsayin CDS.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com