ADC Ta Aika Sako Mai Zafi ga Tinubu kan Sauya Hafsoshin Tsaro
- Jam'iyyar ADC ta nuna shakku kan sauya hafsoshin tsaron da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi
- ADC ta bukaci shugaban kasan ya fito fili ya gayawa 'yan Najeriya gaskiyar dalilan da suka sanya ya dauki wannan matakin
- Jam'iyyar ta nuna cewa sauyin na zuwa ne bayan an yada jita-jitar yunkurin yin juyin mulki a kasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta nemiBola Ahm ed Tinubu ya bayyanawa ’yan Najeriya gaskiyar dalilan da suka sa aka canja hafsoshin tsaro cikin gaggawa.
Shugaba Bola Tinubu dai ya kori hafsoshin tsaro tare da maye gurbinsu da sababbi a ranar Jumma'a, 24 ga watan Oktoban 2025.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar wadda aka sanya a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ADC ta ce kan sauya hafsoshin tsaro?
Bolaji Abdullahi ya nuna damuwa kan yadda sauyin ya zo bayan jita-jitar yunkurin juyin mulki da aka ruwaito a kwanakin baya.
"Ko da yake mun amince cewa shugaban kasa yana da cikakken iko a matsayinsa na kwamandan rundunonin sojoji na yin irin wannan sauyi idan ya ga dama, abin damuwa shi ne cewa hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin yunkurin juyin mulki."
- Bolaji Abdullahi
Jam’iyyar ta kuma ce amsoshin da gwamnati ke bayarwa game da jita-jitar juyin mulki sun nuna rudani da rashin gaskiya, a maimakon a fito da cikakken bayanin da zai tabbatar da kwanciyar hankali.
“Mun lura cewa kusan dukkanin shugabannin tsaron da aka sauya an nada su ne shekaru biyu da watanni hudu da suka gabata, kuma babban hafsan tsaron kasa an nada shi a matsayin hafsan sojojin kasa shekara daya da ta gabata."

Kara karanta wannan
Magana ta fito: Fadar shugaban kasa ta fadi dalilin Tinubu na korar hafsoshin tsaro
"Wannan sauyi yana da illoli masu zurfi ga daidaiton rundunonin tsaro, don haka ba zai yiwu a dauki irin wannan mataki ba tare da dalilai masu karfi ba."
- Mallam Bolaji Abdullahi
ADC ta bukaci Tinubu ya yi bayani
Jam’iyyar ta ce gwamnatin tarayya na da hakkin bayyana wa ’yan kasa abin da ya faru a zahiri, domin tabbatar da gaskiya da kwanciyar hankali a kasar nan.
"A bayyane yake cewa gwamnatin Tinubu ta fara karkacewa daga muhimman lamura. Tsaro na tabarbarewa, ’yan ta’adda na dawowa a wasu yankuna, kuma ’yan bindiga na ci gaba da mamaye wasu sassa na kasar nan."
- Mallam Bolaji Abdullahi

Source: Facebook
Jam’iyyar ta zargi gwamnati da mayar da hankali kan siyasar ci gaba da mulki maimakon kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa, tana mai cewa sauyi a jagorancin rundunonin sojoji zai kara haifar da jita-jita da hasashe a tsakanin jama’a.
"Muna sake jaddada matsayarmu cewa dole ne gwamnatin tarayya ta fito fili ta bayyana gaskiyar abin da ke faruwa, ta kuma tabbatar wa ’yan Najeriya cewa dimokuradiyyarmu ba ta cikin hadari."
- Mallam Bolaji Abdullahi
'Yan Najeriya na son sanin gaskiya
Salisu Bello ya shaidawa Legit Hausa cewa tabbas 'yan Najeriya na son sanin ainihin dalilin da ya sanya aka kori hafsoshin tsaron.
"Tabbas ruwa ba ya tsami banza, yadda aka kori hafsoshin tsaron nan cikin gaggawa ya nuna cewa akwai wani abu a kasa."
"Ya kamata a fito a gayawa 'yan Najeriya gaskiya. A ganina korar da aka yi musu na da nasaba da batun yunkurin juyin mulkin da ake ta yi."
- Salisu Bello
Tinubu ya gana da sababbin hafsoshin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya labule da sababbin hafsoshin tsaro.
Shugaba Tinubu ya gana da sababbin hafsoshin tsaron ne a fadarsa da ke Aso Rock Villa, jim kadan bayan ya sanar da nadinsu.
A yayin taron, Shugaba Tinubu ya bukaci sababbin hafsoshin tsaron su nuna kwarewa wajen sauke nauyin da aka dora musu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

