Janar Undiandeye: Sojan da Ya Tsira da Kujerarsa da Tinubu Ya Kori Hafsoshin Tsaro

Janar Undiandeye: Sojan da Ya Tsira da Kujerarsa da Tinubu Ya Kori Hafsoshin Tsaro

  • Shugaba Bola Tinubu ya sauya hafsoshin tsaro, amma ya bar Manjo Janar Emmanuel Akomaye Parker Undiandeye a mukaminsa
  • Sauyin ya zo bayan jita-jitar yunkurin juyin mulki, inda Shugaba Tinubu ya ce matakin zai ƙarfafa tsarin tsaron ƙasar Najeriya
  • A wannan rahoto, Legit Hausa ta zakulo muhimman abubuwa game da Janar Undiandeye, ƙwararren jami’in leƙen asirin ƙasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja — Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar nadin sababbin hafsoshin tsaro na Najeriya a ranar Juma’a, 24 ga Oktoba, 2025.

Sai dai abin mamaki, Tinubu bai sallami Manjo Janar Emmanuel Akomaye Parker Undiandeye, wanda ke matsayin hafsun rundunar leken asiri na kasa (CDI) ba.

Tinubu ya kyale Janar Undiandeye yayin da ya sallami hafsoshin tsaro.
Hoton Manjo Janar Emmanuel Akomaye Parker Undiandeye, hafsun rundunar leken asiri na kasa (CDI) ba. Hoto: @presidentayollc
Source: Twitter

Tinubu ya sauya hafsoshin tsaro

A sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya nada Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon hafsun tsaron ƙasa (CDS), wanda ya maye gurbin Janar Christopher Musa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da sababbin hafsoshin tsaron Najeriya a Aso Rock

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sababbin hafsoshin sun haɗa da Manjo Janar W. Shaibu a matsayin hafsun rundunar sojojojin ƙasa, Air Vice Marshal S.K. Aneke a matsayin hafsun rundunar sojan sama, da Rear Admiral I. Abbas a matsayin hafsun rundunar sojojojin ruwa.

"Manjo Janar E.A.P. Undiandeye zai ci gaba da kasance wa hafsun rundunar leken asiri na kasa."

- Bayo Onanuga.

Tinubu: “Za mu karfafa tsaron kasa”

A cikin wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na X, Shugaba Tinubu ya ce sauya hafsoshin tsaro ya biyo bayan bukatar ƙara ƙarfin tsarin tsaron ƙasa.

Mun ruwaito cewa, Shugaba Tinubu ya ce:

“Ina umartar sababbin hafsoshin tsaro su ƙara nuna ƙwarewa, himma da haɗin kai a rundunonin soja yayin da suke hidima ga ƙasa cikin mutunci."

Sauyin ya biyo bayan jita-jitar yunkurin juyin mulki da aka ce wasu jami’an soja sun shirya, wanda hedkwatar tsaro ta ƙaryata, kamar yadda muka ruwaito.

Wanene Manjo Janar Undiandeye?

Kara karanta wannan

Tinubu da kansa ya yi magana, ya bayyana dalilin korar hafsoshin tsaron Najeriya

Manjo Janar Emmanuel Akomaye Parker Undiandeye, ɗan asalin Bedia ne a ƙaramar hukumar Obudu, jihar Cross River.

An fara naɗa shi a matsayin hafsun rundunar leken asiri na kasa a ranar 19 ga Yuni, 2023, makonni kaɗan bayan Tinubu ya hau mulki.

Shi ne mutum na biyu daga Bedia da ya kai matsayin Janar mai tauraro biyu, bayan Rear Admiral Peter Agba wanda ya yi ritaya a 2018.

Kafin wannan mukami, Undiandeye ya kasance kwamandan cibiyar ba da horo kan shugabanci da zaman lafiya ta Martin Luther Agwai da ke Jaji, jihar Kaduna.

Janar Undiandeye ya kasance kwararren jami'in leken asiri
Hoton Manjo Janar Emmanuel Akomaye Parker Undiandeye, hafsun rundunar leken asiri na kasa (CDI) ba. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Ƙwararren jami’in leken asiri

Manjo Janar Undiandeye na daga cikin rundunar leken asiri ta sojojin ƙasa, kuma ya yi suna wajen gudanar da aikin leken asiri da dabarun tsaro.

Ya kasance ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar ƙasashe masu ba da hayar sojoji ga Majalisar Dinkin Duniya, waɗanda suka hada rundunar sojojojin kasar Majalisar Dinkin Duniya (UNIBAM) a 2020.

A matsayin sa na hafsun leken asiri, yana kula da hadin gwiwar bayanan tsaro tsakanin rundunonin sojoji, da kuma samar da ingantaccen bayanin leken asiri don tallafa wa yaki da ta’addanci.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Namijin kokarin da Janar Shuaibu ya yi kafin zama hafsan sojojin kasa

Ci gaba da kasance wa a kan wannan kujera ya nuna amincewa da kwarewa da jajircewarsa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a ƙasar.

Namijin kokarin sabon hafsun sojojin kasa

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Manjo Janar Waidi Shuaibu a matsayin sabon hafsun sojojin kasa.

Rahoto ya nuna cewa Janar Shuaibu ya samu nasarori da dama a lokacin da yake jagorantar dakarun Operation Hadin Kai a Arewacin Najeriya.

Rahoto ya nuna cewa rundunar OPHK da Janar Shuaibu yake jagoranta ta hallaka ’yan ta’adda 567, ta kwato makamai 492 da harsasai fiye da 10,000.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com