Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Sababbin Hafsoshin Tsaron Najeriya a Aso Rock
- Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin sababbin manyan hafsoshin sojojin Najeriya da ya nada a fadar shugaban kasa da ke Abuja
- A yau Juma'a, 24 ga watan Oktoba, 2025, Bola Tinubu ya kori hafsoshin tsaron kasar nan tare da nada wadanda za su maye gurbinsu nan take
- Shugaba Tinubu ya bukaci hafsoshin sojin su ba mara da kunya ta hanyar nuna wa jama'a cewa sun cancanci wannan matsayi da aka ba su amana
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawa ta farko da sabbbin manyan hafsoshin tsaro na kasar nan da ya nada a yau Juma'a, 24 ga watan Oktoba, 2025.
Idan ba ku manta ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauke manyan hafsoshin tsaron kasar nan ciki har da babban hafsan tsaro na kasa (CDS), Janar Christopher Musa.

Source: Twitter
Bola Tinubu ya canza Hafsoshin tsaro
Daily Trust ta ce mai girma shugaban kasar ya bar Janar Olufemi Oluyede a gwamnati amma ya sauya masa matsayi daga Babban Hafsan Sojojin Ƙasa zuwa Babban Hafsan Tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma, Manjo Janar W. Shaibu shi ne ya zama sabon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, yayin da Air Vice Marshal S.K. Aneke ya zama Babban Hafsan Sojin Sama.
Bugu da kari, Bola Tinubu ya kuma nada Rear Admiral I. Abbas a matsayin Babban Hafsan Sojin Ruwa, yana mai cewa wannan sauye-sauye sun fara aiki nan take.
Hafsohin tsaro sun yi zama da Bola Tinubu
Jim kadan bayan fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwar wannan gyara da Tinubu ya yi, sababbin manyan hafsoshin tsaron suka kai ziyara Aso Rock.
Shugaba Tinubu ya karbi bakucin shugabannin hukumomin tsaro, kuma aun gana a fadar shugaban kasa duk da ba a bayyana abubuwan da suka tattauna ba kawo yanzu.
A taron, Bola Tinubu ya bukaci hafsoshin tsaron da su tabbatar sun cancanci amanar da aka damka masu ta hanyar ƙara nuna ƙwarewa, himma da haɗin kai, waɗanda su ne ginshiƙan da rundunonin sojojin Najeriya ke alfahari da su.
Ya kuma jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron ƙasa da zaman lafiya a sassan Najeriya.
Wannan ne haduwar farko da shugaban Najeriyan ya yi da su kuma wannan shi ne karo na biyu da ya canza hafsoshin tsaro bayan hawa mulki.
Lamarin ya zo ne a lokacin da ake ta rade-radin cewa an yi yunkurin yin juyin mulkin da zai kawo karshen gwamnatin farar hula ta Bola Tinubu.
Hafsun tsaro 1 ya tsira da matsayinsa
Kamar yadda tuni rahotanni suka gabata, sauya hafsoshin tsaron Najeriya da aka yi bai shafi Janar E.A.P Undiandeye ba.
Janar Emmanuel Undiandeye shi ne CID, wanda aka nada tun a 19 ga Yunin 2023 kuma Bola Tinubu bai fatattake shi.
Legit Hausa ta zakulo bayanai game da Undiandeye, sojan da ya tsira da kujerarsa bayan sauyin da aka samu a gidan tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

