Wata Sabuwa: An Kama Dalibin Jami'ar IBB saboda Sukar Gwamna a Facebook
- Wani dalibin Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBUL) ya jefa kansa a matsaya bayan ya soki Gwamna Umaru Bago a Facebook
- Dakarun rundunar yan sanda sun kama dalibin mai suna Abubakar Isah Mokwa bisa zargin aikata laifuffuka ta yanar gizo
- Wannan ba shi ne karon karon farko da irin haka take faruwa kan sukar gwamnatin jihar Neja karkashin Gwamna Umaru Bago ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lapai, Jihar Neja – Rundunar ’yan sandan jihar Neja ta kama wani ɗalibi da ke karatun digiri na biyu a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBUL) mai suna Abubakar Isah Mokwa.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar da El Rufai ya koma ta rikice, an kori shugaban SDP da wasu jiga jigai 2
Dakarun 'yan sanda sun cafke dalibin ne bisa zargin sukar Gwamna Mohammed Umaru Bago a shafin sada zumunta.

Source: Facebook
An kama dalibin jami'ar IBB a Neja
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Abubakar dai na karatun digiri na biyu watau Masters a Sashen Tattalin Arzikin Noma da Faɗaɗa Ilimin Noma a Jami'ar IBB da ke Lapai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun tabbatar da cewa an kama shi ne a masaukinsa da ke wajen harabar jami’a a Lapai ranar Alhamis da daddare.
Rahotanni sun nuna cewa ɗalibin ya wallafa wasu kalamai na sukar ayyukan Gwamna Bago a Facebook, wanda hakan ya kai ga kunnen gwamnatin Neja.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da kama dalibin ga manema labarai.
Me yasa aka kama Abubakar Isah?
Ya ce an kama Abubakar ne bisa zargin cin zarafi ta yanar gizo, bin diddigin mutane ta kafar intanet, da wasu laifuka da suka shafi aikata laifuka ta yanar gizo.
A cewar SP Abiodun:
“Rundunar ’yan sandan jihar Neja ta karɓi ƙorafi na aikata laifuffukan da suka shafi cin zarafi da bin diddigi ta yanar gizo kan Abubakar Isah, mai shekaru 29, dan garin Mokwa, wanda dalibi ne a jami’ar IBBUL.”
“Bisa haka aka gayyace shi, sannan aka kama shi a Lapai ranar 23 ga Oktoba, 2025, da misalin ƙarfe 11:00 na dare, aka kuma tura shi zuwa hedikwatar rundunar ’yan sanda a Minna domin ci gaba da bincike.”
“Yanzu haka yana hannunmu, kuma za mu sanar da ƙarin bayani nan gaba."

Source: Twitter
Neja: An koka da abin da ke faruwa
Wannan ba shi ne karo na farko da gwamnatin Jihar Neja ta shiga kanun labarai saboda kama masu sukarta ba, cewar rahoton AIT TV.
A watan Agusta, gwamnatin ta dakatar da tashar rediyo mai zaman kanta, Badegi 90.1 FM, wacce ke aiki a Minna, saboda watsa rahotanni da suka soki Gwamna Bago.
Haka kuma, ƙungiyar International Press Institute (IPI) Nigeria ta bayyana damuwa kan irin yadda ake takura wa ’yan jarida da masu sukar gwamnati a karkashin mulkin Gwamna Bago.
Gwamna Bago ya biya wa dalibai kudin rijista
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, ya biya kudin rijistar sababbin daliban Jami’ar Abdulkadir Kure da ke Minna n zangon karatun 2024/2025.
Gwamna Bago ya bayyana haka ne yayin bikin rantsar da sababbin daliban jami’ar 809, inda ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da daukar matakan inganta ilimi.
Bugu da kari, Mai girma gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta fara shirin tura dalibai kasashen waje domin neman ilimi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

