Bayan Kirkirar Sababbin Masarautu, Gwamna Ya Nada Yayansa Sarki a Bauchi
- Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya nada sababbin sarakuna a jihar bayan kirkirar masarautu a kwanakin nan
- Sanata Bala Mohammed ya naɗa ɗan’uwansa, Alhaji Adamu Mohammed, a matsayin sabon Sarkin masarautar Duguri
- A wurin bikin miƙa takardar naɗe, sabon Sarkin Duguri da na Bununu sun gode wa Gwamna Bala tare da alƙawarin bin doka da goyon bayan gwamnati
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya naɗa sababbin sarakunan gargajiya a jihar bayan kirkirar karin masarautu a kwanan nan.
Gwamnan ya nada babban yayansa, Alhaji Adamu Mohammed, a matsayin sabon Sarkin masarautar Duguri da aka ƙirƙira kwanan nan.

Source: Facebook
Daily Trust ta ce sakataren gwamnatin jihar, Aminu Hammayo, ne ya mika takardar naɗe a madadin Gwamnan a fadar Sarkin Duguri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Bala ya kirkiri sababbin masarautu
Hakan na zuwa ne bayan gwamnan jihar ya kirkiri sababbin masarautu domin inganta shugabanci da samar da ingantaccen shugabanci.
Gwamna Bala Mohammed ya sanya hannu kan dokar sababbin masarautu 13 da hakimai 111 a fadin jihar Bauchi.
Ya kuma soke tsohuwar masarautar Sayawa, ya kafa masarautar Zaar da hedkwatarta a Mhrim Namchi, Tafawa Balewa, cewar rahoton The Guardian.
Har ila yau, gwamnan ya gargadi masu siyasantar da doka, ya kuma rattaba hannu kan dokar fansho da karin kasafin kudi na 2025.

Source: Facebook
An yi bikin nadin sababbin sarakuna a Bauchi
An gudanar da nadin a Masarautar Duguri na cikin karamar hukumar Alkaleri a ranar Juma’a 24 ga watan Oktobar shekarar 2025 da muke ciki.
A wajen taron, Hammayo ya roƙi sabon Sarkin da ya ci gaba da mara wa shirye-shiryen gwamnati baya domin cigaban al’umma da dorewar zaman lafiya.
Sabon Sarkin Duguri, ya gode wa Gwamna Bala bisa wannan karamci, yana roƙon Allah ya saka masa da alheri tare da yin alƙawarin biyayya ga gwamnati.
Sarkin Bununu ya karbi takardar nadin sarauta
Haka kuma, Sakataren Gwamnatin ya mika takardar naɗi ga sabon Sarkin masarautar Bununu, Alhaji Jibrin D. Hassan, wanda aka nada su a lokaci guda.
Hammayo ya shawarci sabon Sarkin Bununu da ya tabbatar da bin doka, haɗin kai tsakanin kabilu da samar da zaman lafiya a yankinsa.
Sabon Sarkin Bununu ya gode wa Gwamna Bala bisa amincewa da shi, yana mai tabbatar da cewa ba zai taɓa rusa amanar gwamnati da jama’a ba.
Gwamna Bala ya musanta fita daga PDP
Mun ba ku labarin cewa Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya tabo batun yiwuwar ficewa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.
Shugaban na kungiyar gwamnonin PDP, ya yi nuni da cewa ba zai iya ficewa daga jam'iyyar ta adawa ba inda ya ba yan jam'iyyar tabbaci kan inganta ta.
Gwamna Bala ya nuna cewa akwai hannun wasu kan kokarin kawo rarrabuwar kawuna a jam'iyyar PDP domin farraka ta wanda ya ce za su yi duk mai yiwuwa don dakile haka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

