Tinubu da Kansa Ya Yi Magana, Ya Bayyana Dalilin Korar Hafsoshin Tsaron Najeriya
- An naɗa Janar Oluyede, Manjo Janar Shaibu, AVM Aneke da Rear Admiral Abbas a matsayin sababbin hafsoshin tsaro
- Shugaba Bola Tinubu ya yi godiya ga tsohon CDS, Christopher Musa tare da ba sababbin hafsoshin tsaron umarni
- ’Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu, inda suka danganta sauyin da jita-jitar juyin mulki da aka samu a kwanan nan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja — Shugaba Bola Tinubu ya sanar da babban sauyi a tsarin shugabannin rundunonin tsaro na ƙasar, inda ya kori hafsoshin tsaro da nada sababbi domin ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Jumma’a, 24 ga Oktoba, 2025, Shugaba Tinubu ya tabbatar da naɗin Janar Olufemi Oluyede a matsayin shugaban tsaron Ƙasa (CDS).

Source: Twitter
Tinubu ya sauya hafsoshin tsaron Najeriya
Sanarwar da Shugaba Tinubu ya wallafa a shafinsa na X, ta nuna cewa Janar Olufemi Oluyede zai maye gurbin Janar Christopher Musa.
Sauran sababbin hafsoshin tsaron sun haɗa da Manjo Janar Waidi Shuaibu a matsayin hafsun rundunar sojojin kasa, Air Vice Marshal S.K. Aneke a matsayin hafsun sojojojin sama, da Rear Admiral I. Abbas a matsayin hafsun sojojin ruwa.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuma sanar da cewa Manjo Janar E.A.P. Undiendeye zai ci gaba da rike mukamin hafsun sashen leken asiri na tsaro (CDI).
Dalilin Tinubu na sauya hafsoshin tsaro
Shugaban kasar ya bayyana cewa wannan sauyin “na da nufin ƙarfafa tsarin tsaro na ƙasa” tare da tabbatar da haɗin kai da nagartar jagoranci a cikin dakarun Najeriya.
“Na amince da canje-canje a tsarin shugabannin rundunoninmu domin ƙara ƙarfafa tsarin tsaro na ƙasa.
“Ina godiya ga Janar Christopher Musa da tsofaffin shugabannin tsaro saboda sadaukarwarsu. Ina kira ga sababbin hafsoshi su nuna ƙwarewa, aiki tukuru da kuma haɗin kai tsakaninsu.”
- Shugaba Bola Tinubu.
Sauyin ya zo ne a lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubalen tsaro daban-daban — daga ta’addanci a Arewa maso Gabas, fashi da makami a Arewa maso Yamma, zuwa satar man fetur a Kudu maso Kudu.

Source: Twitter
Martanin 'yan Najeriya kan sauya hafsoshin tsaro
’Yan Najeriya da dama sun tofa albarkacin bakinsu a karkashin sanarwar da Tinubu ya yi a X:
@ADCVanguard_ ya ce:
“Mataki ne mai kyau. Amma ya kamata sababbin shugabannin sojoji su fara aiki da gaggawa, domin ’yan ƙasa sun gaji da kukan rasa masoyansu.”
@isah_muaaz ya ce:
“Sauyin shugabannin soja yawanci yana zuwa kafin babban farmaki ko babban sauyin siyasa. Tun da ba zaɓe ne ke gabatowa ba, akwai wani boyayyan abu a cikin lamarin nan.”
@yngnotorious ya ƙara da cewa:
“Babu bikin ’yancin kai, ga jita-jitar juyin mulki, sannan yanzu an sauke shugabannin sojoji — duka a cikin wata guda. Lamarin yana da ban mamaki.”
Wasu kuma sun bukaci sababbin shugabannin da su dawo da amincewar jama’a ga rundunar tsaro.
An karyata yunkurin juyin mulki
A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojojin Najeriya sun yi karin haske game da jita-jitar da ke cewa an yi yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu.
Hedikwatar tsaron Najeriya ta kuma karyata jita-jitar cewa soke bikin cika shekara 65 da samun ‘yancin kai ya samo asali ne daga yunkurin juyin mulki.
Wannan ba shi ne karon farko da ake yada irin jita-jitar ba, a baya ma an sha kiran sojoji da su yi gaggawar kifar da gwamnatin Tinubu saboda kuncin da ake ciki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


