Sunayen Sababbin Hafsoshin Tsaro da Tinubu Ya Nada bayan Korar Su Janar Musa
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sallami hafsoshin tsaron Najeriya, illa Manjo Janar E.A.P Undiendeye da aka bari a mukaminsa
- An ruwaito cewa, Tinubu ya sallami hafsan tsaron kasa, hafsan sojojin kasa, hafsan sojojin sama da hafsan sojojin ruwa a lokaci guda
- Sababbin hafsoshin tsaron da Tinubu ya nada sun hada da Janar Olufemi Oluyede, wanda ya maye gurbin Janar Christopher Musa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Juma'a, 24 ga watan Oktoba, 2025, Shugaba Bola Tinubu ya kori hafsoshin tsaron Najeriya tare da maye gurbinsu da wasu.
Wannan garambawul na zuwa ne jim kadan bayan da jita jita ta karade Najeriya cewa wasu sojoji na yunkurin kifar da Gwamnatin Tinubu, jita-jitar da tuni aka karyata.

Source: Twitter
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa sanarwar sauya hafsoshin tsaron da misalin karfe 3:15 na ranar Jumu'a a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Babu dadin ji: An tsinci gawar soja a wani irin yanayi bayan bin 'dan bindiga' cikin daji
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, Bayo Onanuga ya ce Shugaba Tinubu ya yi wadannan sauye sauyen ne a bangaren tsaro domin inganta tsaron kasar Najeriya baki daya.
Sunayen hafsoshin tsaron da aka sallama
Daga cikin hafsoshin tsaron da aka sallama, akwai Janar Christopher Musa, wanda yake rike da mukamin babban hafsan tsaro na kasa (CDS).
Sannan Tinubu ya sallami hafsan sojojin kasa, Laftanal Janar Olufemi Oluyede, wanda ya gaji Laftanal Janar Taoreed Lagbaja, wanda ya mutu a ofis a Nuwambar 2024.
Baya ga haka an yi waje da hafsan sojojin sama, Air Marshal Hassan Bala Abubakar, sannan ya sallami hafsan sojojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla.
Sunayen sababbin hafsoshin tsaron Najeria
- Janar Olufemi Oluyede - Hafsan tsaron kasa
- Major-General W. Shaibu - Hafsan sojojin kasa
- Air Vice Marshall S.K Aneke - Hafsan sojojin sama
- Rear Admiral I. Abbas - Hafsan sojojin ruwa
Amma sanarwar ta ce, shugaban kasa bai canja hafsan tsaro na bangaren leken asiri ba, watau Manjo Janar E.A.P Undiendeye.

Kara karanta wannan
Magana ta kare: Babban hafsan tsaro ya fadi lokacin kawo karshen 'yan bindiga, Lakurawa

Source: Twitter
Bukatar Tinubu ga sababbin hafsoshin tsaro
A cikin sanarwar, Bayo Onanuga ya rahoto cewa:
"Shugaban kasa, wanda shi ne babban hafsan rundononin soji gaba daya, ya mika sakon godiyarsa ga hafsoshin tsaron da aka sallama.
"Tinubu ya yi godiya sosai ga namijin kokarin su Janar Christopher Musa da sauran hafsoshin tsaro, bisa yadda suka jajurce wajen yi wa kasa hidima."
Sanarwar ta ce Tinubu ya bukaci sababbin hafsoshin tsaron da su sauke nauyin da aka dora masu kuma su yi aiki cikin kwarewa, da kuma zama madubi ga jami'an tsaron kasar.
Bayo Onanuga ya ce sallamar tsofaffin hafsoshin tsaron da kuma nadin sababbin hafsoshin ya fara aiki nan take.
'Ku tare a Sokoto' - Minista ga hafsoshin tsaro
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan tsaro, Bello Matawalle, ya umurci babban hafsan tsaro na kasa da sauran hafsoshin tsaro da su koma jihar Sokoto.

Kara karanta wannan
Gwamnoni 19 sun hada baki sun yi magana kan mutuwar sama da mutane 40 a jihar Neja
An ruwaito cewa karamin ministan ya dauki wannan matakin ne da nufin ƙara tsananta ayyukan soji a jihar Sokoto domin kawar da barazanar da ‘yan bindiga ke yi.
Umarnin da Matawalle ya bayar, ya jaddada kudirin gwamnati na maido da zaman lafiya da tsaro a jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina, Kebbi da sauransu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng