Majalisar Tarayya za Ta Shiga cikin Lamarin Karin Kudin Gidan Haya

Majalisar Tarayya za Ta Shiga cikin Lamarin Karin Kudin Gidan Haya

  • Majalisar Wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta hada kai da jihohi domin samar da doka kan yadda ake karbar haya a Najeriya
  • 'Dan majalisa daga jihar Cross River, Bassey Akiba, ne ya dauki nauyin kudurin da ya jawo aka kai ga mika bukata ga gwamnati
  • Majalisar ta bukaci a takaita karin haya zuwa abin da bai haura 20% ba, domin saukaka wa masu biyan kudin gidajen haya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Majalisar Wakilai ta bukaci gwamnatin kasar nan da ta hada kai da gwamnatocin jihohi domin tsara doka ta musamman da za ta daidaita kudin haya.

An cimma wannan matsaya bayan tattaunawa a zaman majalisar da aka gudanar a ranar Alhamis, inda aka amince da kudurin dan majalisa daga jihar Cross River, Hon. Bassey Akiba.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya koka kan sabon salon ta'addancin 'yan Boko Haram a Borno

Majalisar wakilai ta yi tsoma baki a kan gidajen haya
Wasu daga cikin 'yan majalisar wakilai Hoto: House of Representatives
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa Hon. Akiba ya bayyana cewa halin tattalin arzikin kasa da ke kara tsananta ya jawo wa mutane, iyalai da ‘yan kasuwa matsanancin hali.

'Yan Majalisa na nema wa 'yan haya sauki

Businessday ta wallafa Hon, Bassey Akiba ya ce a wasu wuraren, farashin haya kan yi tashin gwauron zabo musamman bayan gwamnati ta gina sababbin hanyoyi, kasuwanni ko wasu manyan ayyuka.

'Dan majalisar ya bada misali da wasu unguwanni a Babban Birnin Tarayya Abuja, inda haya ya tashi daga N800,000 zuwa sama da N2.5m a shekara bayan gina hanyoyi a yankin.

Ya bayyana hakan a matsayin matsanancin nauyi ga talakawa, wanda ke iya tura wasu cikin mutane su shiga halin kuncin tattalin arziki ko ma aikata laifi don biyan bukatu.

Hon. Akiba ya jaddada cewa akwai bukatar gaggawa ta daidaita tsakanin hakkokin masu gida da jin dadin masu haya, domin tabbatar da adalci da daidaito a kasar nan.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar mata su karu a majalisa, gwamnoni sun goyi bayan kudiri na musamman

Majalisa ta mika bukata ga gwamnati

Bayan majalisar ta amince da kudurin, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta kara zuba jari a shirye-shiryen samar da gidaje masu araha, domin rage matsin tattalin arziki a kan jama'a.

Majalisa ta mika kudiri ga gwamnatin tarayya
Hoton Shugaban kasa, Bola Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Haka kuma, majalisar ta umarci Ma’aikatar Gidaje da Ci gaban Birane da ta hada kai da gwamnatocin jihohi wajen aiwatar da dokar daidaita haya.

Tana ganin hakan zai taimaka a takaita karin haya kada ya haura 20% duk da karuwar samar da ababen more rayuwa a yankunan.

An kuma umarci kwamitin majalisa kan gidaje da muhalli da ya tabbatar da bin wannan umarni tare da mika rahoto cikin makonni hudu domin daukar matakin doka na gaba.

An jinjinawa majalisa

Wasu mazauna jihar Kano sun yi maraba da yunkurin daidaita yadda ake yawan kara kudin haya a lokutan da suka ga dama.

Mukhtar Lawan ya shaidawa Legit cewa:

"Kwanakin baya, kamar shekara daya ko biyu an yi yayin kara kudin haya. Wasu ya wuce 100%. Gidan abokina da yake biyan N150,000, tashi daya aka yi kari, ya koma N250,000."

Kara karanta wannan

Zaben 2027: ICAN ta yi hangen nesa, ta gano babbar barazana ga darajar Naira

Ya bayyana cewa wannan mataki, idan ya tabbata zai taimakawa jama'a da ke cikin fargabar ƙarin haya.

An buga muhawara mai zafi a majalisa

A baya, mun wallafa cewa an buga muhawara mai zafi a zaman majalisar dattawa na ranar Talata a kan kudirin da ke neman gyara dokar hana zubar da ciki a ƙasar nan.

Rahotanni sun nuna cewa shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, sun shiga cece-kuce kan kudirin.

A karkashin sabuwar shawara a kan dokar, duk wanda ya bayar da magani ko kayan aikin zubar da ciki zai fuskanci hukuncin shekaru 10 a gidan yari babu zabin biyan tara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng