Sulhu Ya Yi Rana: Tubabbun ’Yan Bindiga Sun Sako Mutane Makonni da Sace Su

Sulhu Ya Yi Rana: Tubabbun ’Yan Bindiga Sun Sako Mutane Makonni da Sace Su

  • Al'ummar jihar Katsina na ci gaba da ganin amfanin sulhu bayan wasu tubabbun yan bindiga sun sako mutane
  • Yan bindigar sun saki mutum 19 da suka yi garkuwa da su a Katsina, bayan tattaunawar zaman lafiya karkashin shirin 'Operation Safe Corridor'
  • Hukumomi suka ce ana duba lafiyar wadanda aka sako a cibiyar lafiya ta Haske, Sabuwa, kafin maida su wurin iyalansu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sabuwa, Katsina - Wasu mazauna jihar Katsina sun yaba da ci gaban da aka samu bayan tattaunawa da yan bindiga a yankin.

Mutum 19 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Katsina sun samu ‘yanci bayan tattaunawar zaman lafiya ta 'Operation Safe Corridor Initiative'.

Tubabbun yan bindiga sun saki mutane a Katsina
Yan bindiga yayin shirin sakin mutane a Katsina. Hoto: Dikko Umaru Radda, @ZagazOlamakama.
Source: Twitter

Rahoton Zagazola Makama ne ya tabbatar da haka a cikin wani rubutu a shafin X a yau Juma'a 24 ga watan Oktobar 2025.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga ke shiga Kano daga Katsina suna kai hare hare kan jama'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu yankuna sun yi sulhu da yan bindiga

Al'ummomi da dama a jihar Katsina daga wasu ƙananan hukumomi sun yi zama da yan bindiga domin neman hanyar dakile hare-hare.

Sai dai hakan na samun korafi daga wasu duba da irin rashin amana da yan bindigar ke da shi bayan an yi sulhu da su.

Ƙananan hukumomi da dama sun amince da sulhu da yan bindiga tare da yin alƙawura da juna domin rage yawan asarar rayuka da dukiyoyi da ake yi a jihar.

Radda ya magantu kan sulhu da 'yan bindiga

A bangaren gwamnatin jihar, Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya ce ba zai yi sulhu da yan bindiga ba.

Sai dai ya ce al'ummomi da ke amincewa da zama da yan bindigar domin zaman lafiya sun yi ne a karan kansu kuma abin a yaba ne.

Yan bindiga sun sake sakin wasu da suka sace a Katsina
Taswirar jihar Katsina da ke fama da matsalar tsaro. Hoto: Legit.
Source: Original

Sulhu: Yan bindiga sun saki mutane 19

Kara karanta wannan

Gwamna ya kakaba haraji kan masu jana'za, aure da suna? An ji gaskiyar lamari

Wadanda aka sako sun hada da maza da mata daga kananan hukumomin Sabuwa da Funtua, kuma an sako su da safiyar Alhamis a garin Innono Jigo.

Mutanen sun hada da Safaratu Basiru mai shekara 27, Jamila Auwalu mai shekara 22, da wasu mutum 17 da aka rike tsawon makonni da dama.

Jami’an gwamnati da shugabannin al’umma sun karbi wadanda aka sako sannan suka kai su asibiti mai zaman kansa da ke Sabuwa don binciken lafiya.

Bayan haka, an tura su gida domin haduwa da iyalansu, yayin da hukumomi ke ci gaba da sa ido kan yanayin tsaron yankin.

Hukumomin sun ce ana cigaba da kokari wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Katsina ta hanyar sulhu da su.

Sulhu: Bello Turji ya saki mutane da dama

A baya, mun ba ku labarin cewa majiyoyi sun tabbatar da cewa dan ta'adda, Bello Turji ya saki mutum sama da 100 da yake tsare da su a yankin Zamfara.

An tabbatar cewa hakan ya biyo bayan tattaunawa tsakanin jagoran ‘yan bindigar da shugabannin al’umma a jihar.

Kara karanta wannan

Bayan artabu mai zafi, sojoji sun dakile harin Boko Haram da ISWAP a jihohi 2

Hukumomi sun ce suna sa ido sosai don tabbatar da cewa dan ta'addan bai sake daukar makami ba bayan sulhun.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.