Injiniyoyi Sun Ga Kokarin Gwamna Abba, Sun ba Shi Lambar Girmamawa
- Kungiyar Injiniyoyi ta NICE ta yabi salon aikin Gwamna Abba Kabir Yusuf, musamman yadda ya ke sake fasalin jihar Kano
- Wannan dalili ya sa kungiyar ya yi masa kyautar lambar yabo domin karfafa masa gwiwa ya ci gaba da aikin gine-gine a fadin jihar
- Bikin mika masa lambar yabon ya gudana a taron shekara-shekara na NICE wanda aka yi a Kano, inda ƙwararru da dama suka halarta
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kungiyar injiniyoyin ƙasa ta NICE ta ba Gwamna Yusuf shaidar zama don kungiyar don ƙoƙarinsa na musamman wajen haɓaka ababen more rayuwa a jihar Kano.
NICE ta karrama gwamnan ne a lokacin taron shekaru biyu da aka gudanar a birnin Kano, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi gina kasa da sadarwa.

Source: Facebook
Sanarwar da Mai magana da yawun gwamna, Sanusi Bature D-Tofa ya wallafa a Facebbok ta ce Shugaban NICE na kasa, Otunba Ajanaku ne ya mika wa Abba Gida-Gida lambar girmamawan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aikin Abba a Kano ya burge injiniyoyi
Sanarwar ta kara da cewa Ajanaku ya bayyana gwamnan a matsayin “shugaba wanda ya mayar da Kano babbar rukunin gini a Najeriya.

Source: Facebook
Ya kara da cewa Abba Kabir Yusuf ya inganta Kano ta hanyar ayyukan da ke maida hankali kan jama’a da kuma hangen nesa.
A bangarensa, gwamna Abba ya nuna godiyarsa ga NICE saboda wannan karramawa, wacce ya dauka a matsayin karfafa gwiwa.
Ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bin ƙa’idojin aikin injiniya a duk ayyukan more rayuwa a jihar domin samar da aiki mai inganci.
Gwamnan Kano ya jinjina wa NICE
Gwamnan Kano ya bayyana cewa daraja da aka nuna masa za ta zama ƙarfafawa ga gwamnatinsa wajen ƙara himma wajen samar da ingantattun ayyuka.
Ya ce za a zage damtse wajen samar da ingantattun hanyoyi, gadaje, makarantu, asibitoci da sauran muhimman ababen more rayuwa da za su inganta rayuwar al’ummar Kano.
Haka zalika, ya yi alkawarin ci gaba da haɗin gwiwa tare da ƙungiyoyin ƙwararru kamar NICE domin tabbatar da gaskiya da ƙwarewar fasaha a aiwatar da ayyuka.
Ya nanata alkawarin da ya yiwa mutanen Kano na tabbatar da ana samar da ayyuka da dukkanin abubuwan da za su saukaka masu rayuwa a jihar.
An kuma karrama gwamnatin Abba a Kano
A baya, mun wallafa cewa Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Kano, Dr. Dahir M. Hashim, ya bayyana cewa jihar ta samu wannan babban ci gaba a bangaren yanayi.
Ya bayyana cewa an samu wannan nasara ne sakamakon jagoranci na gari daga Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma sababbin matakan da aka ɗauka wajen inganta muhalli.
Jihar Jihar Kano ta samu ci gaba daga matsayi na 35 zuwa na hudu a Najeriya wajen inganta kula da sauyin yanayi, lamarin da ya sa ta gode wa abokan hulda da suke taimaka mata.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

