An Tashi Tawaga domin Matsawa Jonathan Ya Hakura da Takarar 2027

An Tashi Tawaga domin Matsawa Jonathan Ya Hakura da Takarar 2027

  • Ana matsa wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan lamba a kan tsaya wa takarar Shugaban kasa a 2027
  • Tsohon jagoran ‘yan tawaye, Tompolo ne ya jagoranci tawaga ta musamman zuwa wurin tsohon Shugaban kasan
  • Wasu manyan ‘yan yankin Neja Delta sun ce Bola Tinubu ya cancanci wa’adin mulki na biyu saboda ayyukansa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bayelsa – Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan na fuskantar matsin lamba daga manyan ‘yan siyasa da dattawan yankin Neja Delta a kan zaben 2027.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ana ƙoƙarin shawo kansa ya don kada ya ce zai tsaya takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai zuwa.

Ana son kada Jonathan ya ɗaga batun takara saboda Tinubu
Hoton Shugaban kasa, Bola Tinubu da Goodluck Jonathan Hoto: Bayo Onanuga/Goodluck Jonathan
Source: Twitter

Jaridar Punch ta tattaro cewa a maimakon ya yi takara, an so ya mara wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu baya don sake samun wa’adin mulki.

Kara karanta wannan

Dakarun tsaron Najeriya sun harzuka, sun hallaka jagoran 'yan ta'adda a Filato

An aika wa Goodluck Jonathan tawaga

Rahoton ya bayyana cewa tsohon jagoran ‘yan tawaye, Cif Government Ekpemupolo wanda aka fi sani da Tompolo, ne ke jagorantar ƙoƙarin na shawo kan Jonathan.

Tompolo, tare da abokan aikinsa kamar Kestin Pondi da daraktan Tantita Security Services sun mai wa Jonathan ziyara.

An kai ziyarar tare da Joshua Maciver, mataimakin ɗan takarar gwamna na APC a Bayelsa a 2023, inda suka gana a gidansa da ke Otuoke a ranar 16 ga Oktoba, 2025.

An aika tawaga don ta rarrashi Jonathan
Hoton tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Twitter

Wata majiya ta tabbatar da cewa tattaunawar ba ta tsaya ne kan batun tsaro ba kamar yadda wasu jaridu suka ruwaito, illa dai kan siyasa da makomar yankin Neja Delta.

An ce Tompolo ya bayyana wa Jonathan cewa mafi yawan mutanen yankin ba sa son ya sake tsayawa takara, kuma suna ganin Tinubu ne ya fi cancanta ya ci gaba da mulki.

Sakon Tampolo ga shugaba Jonathan

Kara karanta wannan

Abin da Atiku ya ce wa Kwankwaso da ya cika shekaru 69 a duniya

Wani na kusa da Jonathan ya bayyana cewa Tompolo ya jaddada masa irin gudunmawar da Tinubu ya bayar ga yankin — kamar ginin hanyar Lagos–Calabar da jami’ar da aka kafa a ƙasar Ogoni.

A cewarsa, hakan ne yasa suka ga ya dace su mara wa Tinubu baya don ci gaba da ayyukan da ya fara har zuwa 2031.

Tompolo ya kuma ba da shawarar cewa Jonathan ya bi sawun matarsa, Patience Jonathan, da gwamnan Bayelsa Douye Diri, waɗanda suka nuna goyon baya ga Tinubu.

A cewar majiyar, Tompolo ya gargade shi da kada ya yarda wasu ‘yan siyasa su rura masa wuta ya tsaya takara, domin ba zai samu isasshen goyon baya daga gida ba.

Sai dai tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar LP a Bayelsa, Udengs Eradiri, ya ce babu hujja da ke nuna cewa Jonathan na da niyyar tsayawa takara a 2027.

'Yan Arewa sun goyi bayan Jonathan

A baya, kun ji cewa ƙungiyar masu goyon bayan Jam’iyyar PDP a Arewa da aka gudanar a Birnin Kebbi daga 8 zuwa 9 ga watan Oktoba 2025 don nuna goyon baya ga Jonathan.

Kara karanta wannan

2027: Peter Obi ya magantu kan fafatawa da Atiku domin neman tikitin ADC

Kungiyar ta bayyana Jonathan a matsayin mutum mafi dacewa domin ya farfado da martabar jam’iyyar PDP a ƙasar nan domin ta farfado daga halin da take ciki a yanzu.

Duk da cikakken goyon bayansu ga Jonathan, Ƙungiyar Arewa ta nuna damuwa kan wasu fitattun shugabannin PDP da take zargi da yin aiki tare da jam'iyyar APC mai mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng