Karya Ta Kare: Sojoji Sun Kama Rikakken Dan Bindiga, Babawo Badoo
- Sojojin Najeriya sun kama fitaccen jagoran ta’addanci Idris Idris wanda aka fi sani da Babawo Badoo a Filato
- Dakarun sun kuma kama wasu mutum 37 tare da ceto mutane 15 da aka yi garkuwa da su a fadin kasar nan
- Sojojin sun kuma kashe ‘yan ta’adda biyu tare da kwato makamai, harsasai da wasu kayayyaki masu daraja
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta samu nasara a yaki da ta’addanci bayan cafke fitaccen jagoran ‘yan ta’adda, Idris Idris, wanda aka fi sani da Babawo Badoo.
Baya ga Badoo, sojojin sun kama wasu mutum 37 a yayin ayyukan hadin gwiwa da aka gudanar a sassan kasar nan.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa rundunar tsaro ta ce sojoji sun ceto mutane 15 da aka yi garkuwa da su, yayin da aka kashe wasu ‘yan ta’adda biyu a fafatawar da aka yi da su.
Sojojin sun ce an samu nasarar kwato makamai da harsasai iri-iri, da sauran kayayyaki da ‘yan ta’addan ke amfani da su wajen kai hare-hare da yin garkuwa da mutane.
Sojoji sun cafke Babawo Badoo
Rahoton ya nuna cewa an kama Babawo Badoo ne a ranar 20, Oktoba, 2025, a kauyen Lugere da ke karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato, bayan jami'an tsaro sun samu bayanan sirri.
Sojojin Operation Enduring Peace ne suka kaddamar da samamen tare da kama shi da bindiga kirar AK-47, harsasai, waya da kuma N12,000.
Majiyar sojojin ta bayyana cewa Babawo Badoo ya shahara wajen kai hare-hare da sace mutane a yankin Arewa ta Tsakiya, kuma yana da hannu wajen aikata manyan laifuffuka.
An cafke karin mutum 19 a Bassa
Bugu da kari, dakarun Operation Enduring Peace, tare da hadin gwiwar ‘yan sanda da jami’an CJTF, sun kai samame a kauyen Saya da ke karamar hukumar Bassa.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa dakarun sojojin sun kama mutum 19 da ake zargi da hannu a ta’addanci.
An ce ana bincike a halin yanzu domin gano yadda suke da alaka da wasu manyan laifuffuka da ke faruwa a yankin.
Rahotanni sun ce aikin na daga cikin matakan da sojoji ke dauka don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar Filato da kewaye.
Sojoji sun kashe masu garkuwa da mutane
A wani samen dabam, dakarun rundunar sojoji tare da hadin gwiwar JTF sun kashe ‘yan bindiga biyu a karamar hukumar Kanam.

Source: Facebook
Hakan na zuwa ne bayan gudanar da samame a kauyuka hudu — Kukawa, Shuwaka, Ganjuwa da Tunga — bayan ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane a hanyar Wanka-Dengi.
'Yan bindiga na kai hare-hare Kano
A wani rahoton, man kawo muku cewa wasu al'umma a karamar hukumar Shanono a jihar Kano sun yi korafi kan hare-haren 'yan bindiga.
Mutanen yankin sun ce 'yan bindiga na shigo musu daga Katsina suna garkuwa da mutane, satar shanu da sauransu.
Sun yi kira ga Abba Kabir Yusuf da gwamnatin tarayya da su kai jami'an tsaro yankin domin kare rayuwar mutanensu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


