Yadda 'Yan Bindiga ke Shiga Kano daga Katsina Suna kai Hare Hare kan Jama'a
- Al’ummar karamar hukumar Shanono a jihar Kano sun koka kan yadda ‘yan bindiga ke kai musu hare-hare tun daga shekarar 2022
- Shugaban kwamitin tsaron Faruruwa, Yahaya Umar Bagobiri, ya ce ‘yan bindiga daga jihar Katsina ne ke shigowa suna kashe mutane
- Al’ummar yankin sun roƙi gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta turo jami’an tsaro don kawo ƙarshen ta’addancin da ya addabi jama'arsu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Al’ummar yankin Shanono a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su dauki mataki cikin gaggawa domin dakile hare-haren ‘yan bindiga da suka addabi yankin.
Bayanin da mutanen suka yi ya nuna cewa sun fara fuskantar mutanen yankin ne tun shekaru uku da suka wuce.

Source: Original
Shugaban kwamitin tsaron Faruruwa, Yahaya Umar Bagobiri, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da jaridar Daily Trust a Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun addabi yankin Kano
Bagobiri ya bayyana cewa al’ummar yankin sun fuskanci matsanancin kalubale na tsaro tun daga shekarar 2022, inda ‘yan bindiga ke shigowa da babura fiye da 50 suna kai hari.
Ya ce a wasu lokuta suna kashe mutane, wasu kuma suna yin garkuwa da su ko kuma satar dabbobin da jama’a suka dade suna kiwo.
A cewarsa:
“Mun fuskanci matsalar tsaro mai tsanani tsawon shekaru uku. ‘Yan bindiga daga Katsina ke shigowa Faruruwa da kewaye suna kashe mutane, suna yin garkuwa, suna kuma satar dabbobi.”
Asarar da jama’a suka yi a Kano
Bagobiri ya bayyana cewa a cikin hare-haren da aka kai, an rasa dabbobi da dama ciki har da shanu, awaki, da raguna.
Ya ce:
“Aƙalla shanu 150 ne aka kwashe zuwa yanzu, kuma ‘yan bindigar kan zo da babura fiye da 50 suna satar dabbobi, suna kashe mutane, ko kuma su yi garkuwa.”
Ya ƙara da cewa tun daga shekarar 2022 zuwa yanzu, al’ummar yankin sun rasa fiye da shanu 1,600 da kuma babura da dama da sauran kayayyaki masu daraja.
'Yan Kano sun nemi agajin Tinubu da Abba
Shugaban kwamitin ya yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da kuma gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da su turo jami’an tsaro da za su kare rayukan jama’a.

Source: Facebook
A cewarsa, akwai buƙatar gwamnati ta haɗa kai da jami’an tsaro, musamman sojoji da ‘yan sanda, don dawo da zaman lafiya a yankin.
Halin da yankin ke ciki yanzu a Kano
Bagobiri ya bayyana cewa wasu ƙauyuka da ke kusa da Faruruwa sun zama kufai saboda jama’a sun tsere zuwa jihar Katsina domin neman tsira.
Ya yi gargadin cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, akwai yiwuwar ‘yan bindigar su mamaye dukkan yankunan da ke iyaka tsakanin Kano da Katsina.
Sojoji sun kashe dan bindiga Abu AK
A wani labarin, mun kawo muku cewa dakarun Najeriya sun tabbatar da cewa sun kashe dan ta'adda da ake nema ido rufe, Abu AK.
An kashe Abu AK ne yayin da ya shiga wata kasuwa a jihar Zamfara domin yin sayayya kafin asirin shi ya tonu.
Wata mata ce ta sanar da shigowarsa kasuwar kuma nan take sojoji suka cafke shi, sai dau an harbe shi a lokacin da ya so guduwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


